Wata kotu a yankin Kado da ke Abuja, ta yanke wa wani matashi mai shekaru 24, mai suna Micheal Ayegh, mai shekaru 24 hukuncin daurin watanni 12 a gidan yari, bisa samunsa da laifin hada baki da kuma satar injin janareta wanda kudinsa ya kai N550,000.
Matashin da ya fito daga jihar Nasarawa, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, ya kuma roki kotun da ta yi masa sassauci.
- Zaben Gwamnoni: Wasu Na Kitsa Makarkashiyar Bata Sunan Gwamnan Gombe —APC
- Na Kalubalanci Tsarin Da Ya Ayyana Tinubu A Matsayin Shugaban Kasa -Peter Obi
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Muhammed Wakili ya ce, ya yanke wa wanda ake kara hukunci ne bisa la’akari da laifin da ya yi.
“Kotu ta samu wanda ake tuhuma da aikata laifin, bisa ga rokon da ya yi na a yi masa rangwame, wanda shi ne karon farko da ya yi laifin da bai bata lokacin kotu ba.
“An yanke wa Micheal Ayegh hukuncin daurin watanni 12 a gidan yari tare da zabin biyan tarar N20,000, in ji alkalin.
Lauyan mai shigar da kara, Stanley Nwafoaku, ya roki kotun da ta biya diyya N550,000 kasancewar darajar janaretan da aka sace.
Sai dai alkalin kotun ya amince da bukatar sannan ya umarci wanda aka yanke wa hukuncin biyan diyya N550,000 ga wanda ya kai karar.
Ya ce hukuncin zai zama izina ga masu son aikata duk wani laifi.
Tun da farko dai lauyan mai shigar da kara ya shaida wa kotun cewa, an gurfanar da wanda ake tuhumar ne a kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi hada baki da kuma sata.
Nwafoaku ya ce a ranar 28 ga watan Fabrairu da misalin karfe 9:30 na dare, mai shigar da kara Mista Iheanacho Anayo na yankin Danziyal Plaza Central Abuja, ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Mabushi.
Ya yi zargin cewa a ranar 10 ga watan Fabrairu da misalin karfe 8:30 na dare, wanda ake tuhumar ya hada baki da wani tare da sace janareta mallakin wanda ya kai karar.
Nwafoaku ya ce yayin binciken ‘yan sanda wanda ake kara ya amince da aikata laifin.
Lauyan mai gabatar da kara ya bayyana cewa laifin ya ci karo da tanadin sashe na 97 da 288 na dokar laifuka.