Fasihin mawakin Hausa, kuma dan kasuwar dake dillancin wakokin Hausa a yanar gizo, mai suna Aliyu Abubakar, da ake wa lakabi da Haidar Blog, ya bayyana wannan kyakkyawan fata da buri da yake da shi ne a kan mawaka da dukkan wadanda Allah Ya yi wa baiwar basirar na suna amfanuwa da basirar tasu don kara samun kwarin gwiwa gare su.
Tare kuma da yin kira ga matasa da su kara kaimi wajen neman ilimi, wanda da shi ne rayuwar bawa take yin haske kuma komai ke zuwar masa a saukae, a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu. Ga dai yadda tattaunawarsu da ADAMU YUSUF INDABO ta kasance:
- Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Daina Muzgunawa Kamfanonin Waje
- Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 3 A Wasu Birane
Wane ne Haidar Blogger, cikakken suna da takaitaccen tarihinka?
To a takaice dai asali suna na shi ne Aliyu Haidar Abubakar. Kuma asalina haifaffen Garin Zaria ne, a wata unguwa mai Suna Gyellesu. Na yi makarantar primary har zuwa secondary. Sannan yanzu haka ina ci gaba da karatu na a ABU Zaria. Sunana na Haidar Blog ya samo asali ne tun lokacin da muke secondary saboda ina son Ilimi a kan na’ura mai kwakwalwa wato computer. Don haka sai na kasance mai bincike da bin kwakkafi a kan computer tun wancan lolacin. Hakan ya taimaka min sosai wajen sanin abubuwa da dama da suka shafi computer, har ma na yi wani website mai Suna HaidarBlog a inda nake rubuce-rubucena a kan harkar Entertainment. Toh ka ji Yadda na samo Sunan Haidarblog.
Sunan Haidar Blog sananne cikin mawaka da ma industry, to ya aka yi ka tsinci kanka a cikinsu?
To farkon fara wakena dai na fara ne da yin wakokin yabon fiyayyan halitta (S.A.W.) tun a makarantar Islamiyya. Daga nan kuma son waka ya shiga raina ya zauna daram, har ya kai ni ga shiga cikin mawaka ina kulla abota da su. Don dama ka san ‘yan Hausa suka ce “Ba a abota sai hali ko ra’ayi sun zo daya.”
To wacce waka ka fara rubutawa, kuma cikin tarin wakokin naka wacce ce bakandamiyarka?
To wakar da na fara rubutawa da hannuna ita ce SAYYIDIL ANAMI wacce take ta yabo ce tsantsa ga fiyayyan halitta. Allah Ya sa ya cece mu a ranar da babu wani maceci bayan shi Ameen. Amma wakar da na fara shiga studio na rera ta, ba ni na rubuta ta ba, abokina ‘Ghali Ladabin Bege’ shi ne ya rubuta ta ni kuma na rera. Bakandamiya a cikin tarin wakokina kuwa ita ce wacce na yi mata lakabi da DIWANI.
To ya batum wakokin nanaye, ko na ce wakokin soyayya?
Nakan Rubuta wakokin soyayya, amma dai ba ni nake rerawa ba.
Da alama ka fi karkata ga wakokin yabo. To ya aka yi ka yi kicin-kicin a cikin harkokin wakokin da ba na yabo ba?
Eh Toh ni Mutum ne mai son ganin masu basira Suna amfanuwa da basirarsu. To don haka sai na kutsa ciki. Bincike, na yi binkice na ga da yawan mawakan Arewa ba su san ta ya ya kamata a ce sun amfana da basirarsu ba. To a nan ne na fara binkicen wadanne hanyoyi ne ake samun kudi da waka? Ma’ana yaya za a yi Mawaki ya sayar da wakar sa a Internet, tunda yanzu babu CD, babu cassette. A haka kuma Allah da ikon sa muka yi binkice. Har dai ma na yi makaranta a Online, a kan yadda zan bi wajen Siyar da waka a online daa dai sauransu.
To yanzu ya kasuwancin wakokin yake a yanar gizo, shin ko kwalliya na biyan kudin sabulu?
Eh a gaskiya tana biya, amma ga Wanda ya san yadda zai bi ya samu kudi. Sakamakon da yawan mawakan mu na arewa wasu ba su san yadda na za su Distribution din wakaba. Ballan tana a ce promotions (marketing), ko Music Publishing, ko syc licensing.
To a matsayinku na manyan mawakan dake da ido a kan yadda za a tafi da zamani, ko akwai wani taimako da kuke bawa matasan mawaka musamman ta bangaren marketing a yanar gizo?
Eh sosai ma kuwa. Muna iya yin mu wajen nuna wa da yawansu hanyoyi da ya kamata su bi wajen tallata kansu da hajojinsu ba tare da sun biya ko sisi ta hanyar yanar Gizo. Wasu kuma sukan biya mu mu yi musu Promotion koh kuma mu zama manager dinsu. Ban da haka ma, nakan bayar da courses a online, kamar a zoom meeting da wasu Mawaka Koh kuma. Artist Management. Don yanzu haka Ina Management na Artist kamar Kawu Dan Sarki, Sani Ahmad, Zainab Ambato, Rabil Jo’s. Da dai sauransu. Ma’ana ni ne mai kula da music Distribution, Music publishing, Music copyright, Sync licensing da social media management nasu.
Na ji ka ambaci ‘music publishing’ ka kuma maimaita ta. Wai me take nufi ne?
Music publishing wani abu ne da ake yi wa Maruruta waka da ma mawakan, wajen ganin Kowa ya karbi rabon sa a wannan wakar,kamar yanzu a ce wani dan America ya kunna wakar Hamisu breaker a club Koh gidan Abinci. To in dai su Hamisu Breaker sun yi publishing wakar tasu to za a biya su wannan kudin kunna wakarsu da ya yi. To wadancan mawaka da na lissafa ma a sama, ni ne nake musu publishing wakokinsu shi ya sa a kullum suke kirga ribar wakokim da suka wallafa har na shekarun da suka shude.
Ikon Rabbi, lallai ilimi kogi ne. To daga shigarka wannan harka, ta managing and music publishing zuwa yau wadanne nasarori ka cimma?
Alhamdulilah a wanna harkar ba ni da abin cewa Allah Sai godiya, na samu nasori da yawa, domin na fara wannan aiki ne da wayata ta hannu. Amma yanzu kuma ga shi har ina da Office da yara da muke harkoki tare.
Kuma ya batun kalubale?
Kalubale wannan kuma dukkan wanda ya yi nasara a rayuwa Sai Ya fuskaci kalubale.
Kasancewar harkarku harka ce ta tara masoya. To ta wacce hanya masoyanka za su iya samun ka?
Mutane Suna iya samu na a Shafina da INSTGRAM koh tweeter koh tiktok.
A karshe, wanne kira ko fata za ka yi ga masoyanka da kuma abokan harkarka da mawaka baki daya?
Kira zan yi ga dukkan Samari da mu dage wajen neman ilimi a kan dukkan wata harka da za ka yi, domin in kana da sani a wannan fanni Komai zai zo maka da sauki.
To Malam Haidarblog mun gode.
Ni ne da godiya.