Sannu bata hana zuwa sai dai dade ba a je ba haka dai masu iya magana suke cewa hakika an dade ba a je ba,amma daga karshe dai an je maganar zabubbykan da aka yi tsakanin 25 ga Fabrairu da 18 Maris 2023,da sun shafi na Shugaban kasa ‘yan majalisun kasa.
Bayan kammala su ne sai zaben gwamnoni da ‘yanmajalisun Jihohi da aka kammala ranar Asabar ta makon daya gabata,masu yin murna saboda sun yi nasara sun yi,wadanda kuma suke bakin-ciki ba domin komai ba sai saboda basu samu nasara ba.
- A Karon Farko Iyayena Ba Su Amince Da Shigata Fim Ba —Fatima Moh’d
- Manoman Rani Na Sa Ran Samar Da Shinkafa Da Alkama Mai Yawa A Taraba
Haka ne al’amarin rayuwa yake musamman ma duk abinda aka riga aka sa ma ranar yin shi ko ba dade-ko ba jima sai shi da ranar sun hadu,kamar yadda su ranakun zaben suka zo suka bar wasu cikin mamaki,to mamaki mana domin kuwa abubuwan da ba a tsammani suka faru inda Giwa tayi tuntube ta kuma Kare.Idan dai ba ayi saurin mantawar ba ko shakka babu Giwar tayi tuntuben ta Kare.Abubuwa da yawa sun faru wadanda idan aka bi su sau da kafa za a iya ganewa gaskiya mnayan darussa ne da suka faru wasu sun kasance wata manuniya ce su ‘yan siyasar yadda zasu fuskanci zabubbukan suka kasa ganewa.
Kafin dai a kai ga yin su zabubbukan na shekarar 2023 abin ya fara kasancewa wani abu ne da masu iya magana ke cewa “Kukan Kurciya Jawabi Ne Mai Hankali Ke Ganewa” wato ita maganar kungiyar gwamnonin nan na sassan Kudu maso Kudu,Kudu maso gabas,kudu maso yamma,sai kuma Arewa ta tsakiya, da aka fi sani da G5 data hada da gwamnonin jam’iyyar PDP biyar wadanda aka fi sani da sunan, sai ga shi uku daga cikinsu basu samu biyan bukatar ba domin sun kasa lashe zaben Sanatan da aka yi tare dana Shugaban kasa a kokarinsu na su tafi hanyar yin ritaya daga karshe a harkokin siyasa idan ba wata bace Allah ya bullo da ita cikin rashin sanin masu kokarin zuwa majalisar Dattawa ta kasa.Wannan bayan sun kammala wa’adinsu na shekaru takwas na hudu sau biyu.
Kungiyar G5 ta kunshi gwamnonin PDP biyar Okezie Ikpeazu (Abia), Ifeanyi Ugwuanyi (Inugu), Samuel Ortom (Benuwe), Seyi Makinde (Oyo) da kuma Nyesom Wike na(Ribas).Gwamnonin biyar sun kulla kawancen ko kuma abokantakar ce, sai bayan da aka kammala zaben fidda –gwani na Jam’iyyar PDP a watan Mayu 2022 inda suka nemi Shugaban jam’iyyar na kasa Sanata, Iyorchia Ayu cewa ya sauka daga mukaminsa domin ya bar ma wani daga sashen Kudu da zai maye makwafinsa.Wannan kuma wata shawara ce da suka ba dan takarar jam’iyyar PDP idan ya amince da ita su zasu ba shi goyon baya lokacin zaben Shugaban kasa na 25 ga Fabrairu
Duk Atiku Ayu suka kira wannan ikirarin gwamnonin biyar a matsayin wani wasan yara ne inda suka yi watsi da bukatar tasu ta cewa sai Sanata Ayu ya sauka sannan su marawa Atiku Abubakar baya lokacin zabe.
Kamar sanin kowa ne lokacin zaben Shugaban kasa Atiku Abubakar bai samu nasara ba a duk Jihohin biyar, Atiku,Peter Obi jam’iyyar Labour Party ya samu nasara a Jihohin Enugu Abia, Bola Tinubu na APC ya samu nasara a Jihohin Oyo, Benuwe, da Ribas.
Daga cikin ‘yan kungiyar ta G5,Ortom, Ikpeazu, Ugwuanyi da Wike duk gwamnoni ne masu kammala wa’adinsu na shekaru hudu sau biyu yayin da shi Makinde shi shekara hudu ne yake gab da kammalawa ya tsaya yana neman a sake zaben sa karo na biyu wanda yayi sa’a zai sake komawa gidan gwamnati ya sake maimaita wasu shekaru hudun.An sha yin tarurruka da suka fi shurin masaki saboda sasanta manyan gaggan mutanen biyu Atiku Abubakar da Nyesom Wike amma abin yaci tura,wani abin mamaki ma shi gwamnan yafi kowa tsiwa wanda ke bi ma shi baya shine na Benuwe. Daga karshe shi dama Shugaban jam’iyyar PDP na kasa ko a Jihar ta shi ta Benuwe ba wani abu bane domin sun kasa rufa masa asuri bare shi ma ya rufa ma wani.
Shi yasa Hausawa lalle sun kyauta da suka ce “Kowa Yace Ruwan Wani Ba Zai Tafasa BaTo Shi Nashi Ko Dumi Ba Ya Yi” Shi Wike bai nemi wata dama ta tsaya takarar Sanata ba amma ya san irin tuggun siyasa na ‘yan siyasa daya shirya saboda kuwa ai bayan zaben Shugaban kasa dana ‘yan majalisun kasa, jam’iyyarAPC har godiya ta yi ma shi kan irin gudunmawar daya bata,hakanan ma gwamnan Jihar Benuwe Samuel Ortom da bakinsa ya furta cewa da ace shi ba dan jam’iyyar PDP bane da ya zabi Peter Obi ashe dama manufarsa ce yake fada saboda ai lokacin zaben Shugaban kasa dan takarar na APC ne ya lashe zaben Shugaban kasa da gaggarumar nasara a Jihar da kuri’u 310,468 Peter Obi ya samu 308,372 Atiku Abubakar dantakarar PDP ne ya zama na uku da 130,081 yayin da Kwankwaso yake da 4,740.Idan da ace sun yi PDP zallah sai ya samu kuri’u fiye da 700,000 in babu tuggun ‘yan siyasa domin kuwa ai Jiha ce ta Shugaban jam’iyyar PDP na kasa amma sai ga dantakararta ya zo na uku.Hakika an yi amfani ne da addini da kabilanci matuka a zabubbukan Shugaban kasa dana majalisun kasa idan ba haka ba ai babu yadda za ayi wani dantakarar Shugaban kasa daga sashen Kudu maso gabas har ya shigo Arewa yayi ma ‘yan takarar na Arewa raga-raga abu ne daure kai ma a Arewa ta tsakiya,wannan ba karamin darasi bane kowanne dan siyasa wala babba ko matashi ya dace ya yi koyi da shi zuwa gaba.
Ba abu bane mai kyau ga dan siyasa ya rika kurin cewa shi dole ne ko wanne lokace shi zai cigaba da damawa ko damawa da shi, yin hakan bai yi ma kan shi adalci ba ko kadan,dalili kuwa rami ne ya gina bai san shi ne zai fada ba amma sai ya samu kan shi a ciki,ba kuma wanda zai taimaka wajen dauko shi ya shiga ke nan Shi yasa maraigayi Alhaji Mamman Shata Katsina a wakarsa mai taken “A Gargadi Mai Gina Ramin Mugunta” yace ‘ya kai mai gina ramin mugunta to ka gina daidai kwaurinka watakila kai zaka fada”,amma yawancin masu irin hakan wani wawakeken rami ne mai zurfi suke ginawa wanda duk ya fada gaba daya zai iya shanye shi kamar dai yadda ya faru ga wasu manyan ‘yan siyasa da suka mayar da majalisun Jihohi dana kasa kamar kayan gadonsu ko kuma mallakin kansu.Irin sune suka gina wa kansu ramin muguntar wadda mawaki ya yi gargadin kada su gina shi, maimakon su rika jawo su matasa suna koya masu ga yadda dabarun siyasa suke sannu a hankali sai su koya har watarana suma su fara nuna gwanintarsu,sai ta kasance su ba hakan suke so ba.Ko dai ba magana a zura ido ta ishi mai hankali kamar yadda marigayi Sani Sabulu Kanoma ya fada a wakarsa inda yace, “ In ba a jiran lokaci akwai wahala can gaba’ yace “Na san dan Adam watarana dan Adam halin agaza aggarai,shi zai ishe ka a gida yace maka taso mu je sai kun fara tafiya yace maka ya gaji”.
Wasu ‘yan siyasa anasu ganin ko yaushe su kasance sune na BARA SUNE NA BANA SUNE NA SHEKARAR BASHASHA bayan kuwa al’amarin ai sam ba haka yake ba,Allah shi ne mai kowa mai komai mai yin abinsa inda yaso da lokacin da yaso ya kasance an so abin,dole sai kowa ya jira lokacinsa duk kuma tagumin mutum ai baya wuce habarsa.Idan kuma kai yana da tsoka kamata yayi kowa ya taba na shi ya ji.Daga karshe duk wata turjiyar da za ayi yadda yaso haka abin zai kasance.