Wata Kotu da ke zamanta a birnin Makurdi, ta bai wa Dakta Iyorchia Ayu umarnin daina bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.
Alkalin kotun, Wilfred Kpochi wanda ya bayar da umarnin, ya bukaci Ayu ya janye daga shugabancin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a saurari karar da aka shigar a kansa.
- Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 6 A Wasu Birane
- DSS Ta Cafke Tsohon Soja Da Lauya Da Wasu Kan Zargin Ta’addanci
Tun farko, karar da Injiniya Conrad Utaan ya shigar ta nemi kotu ta hana Ayu daga bayyana kansa a matsayin shugaban PDP kasancewar dakatarwar da aka yi masa.
PDP ta dakatar da Ayu ne bisa zarginsa da wasu ayyuka na cin amanar jam’iyyar.
Shugabannin jam’iyyar a matakin gundumarsa da ke karamar hukumar Gboko, a Jihar Benue ne suka dauki matakin.
Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kada kuri’ar rashin kwarin gwiwa kan ayyukansa.
Tun da farko, Wike na Jihar Ribas da wasu Gwamnoni a Kudu sun bukaci Atiku ya sutale mukamin Ayu, amma ya yi kunnen uwar shegu da su.
Lamarin da ya sanya gwamnonin biyar da ake wa lakabi da G-5 suka ki marawa jam’iyyar baya a zaben shugaban kasa na 2023.