Dan wasan gaba na ungiyar wallon kafa ta Barcelona dake kasar Spain, Robert Lewandowski shi ne kan gaba a yawan cin wallaye a La Liga kawo yanzu a kakar bana inda ya zura wallaye 15 a raga.
Haka kuma tsohon dan wallon Bayern Munich, shi ne kan gaba a yawan kai hare-haren cin wallo a babbar gasar ta Sifaniya mai 41 kuma ranar Asabar za’a ci gaba da wasannin La Liga karawar mako na 28, bayan an kammala fafatawa tsakanin asa da asa a ranakun da FIFA kan ware.
Tun bayan da dan wallon na Poland ya koma Sifaniya da buga wasa kafin a fara gasar bana, mai koyar da ‘yan wasan Barcelona, Dabi, ya ke anfani da shi a gurbin mai cin wallo, sai idan ya ji rauni.
Hakan yana nufin yawan hare-haren da Lewandowski kan kai a La Liga ya ci wallo kaso 36.6 cikin 100 kenan sai dan wasan Real Madrid Karim Benzema, wanda ya lashe kyautar yawan cin wallaye a bara, ya kai hari sau 30 da zura wallo 11 a raga.
Shima dan wasan Real Madrid, Vinicius Junior hari 30 ya kai amma kwallo takwas ya ci kawo yanzu a La Liga sai Enes Unal na Getafe, shine na biyu a yawan cin wallaye a La Liga mai 13, amma hari 28 ya kai a raga kawo yanzu.
Za’a iya cewa kaso 46.4 da dan wasan Getafe ya kai hare-haren, shi ne ya zura kwallo 13 a raga sannan a manyan gasar Turai biyar, Lewandowski shi ne na shida a jerin ‘yan kwallon da ke gaba a kai hare-haren cin kwallaye.
Kylian Mbappe ne kan gaba wanda ya kai hari 58 da Leonel Messi mai 46 dukkansu daga Paris St Germain sai Harry Kane na Tottenham shi ne na uku, wanda ya kai hari 46 da Erling Haaland na Manchester City mai 44 da kuma Jonathan Dabid na Lille mai 40.
‘Yan wasan da ke kan gaba a cin wallaye a La Liga a bana:
Robert Lewandowski Barcelona 15 Enes Unal Getafe 13. Iago Aspas Celta de Bigo 12
Borja Iglesias Real Betis 12. Joselu Espanyol 12. Karim Benzema Real Madrid 11
Albaro Morata Atletico de Madrid 10 Bedat Murii Real Mallorca 10. Aledander Sorloth Real Sociedad 9. Gabriel Beiga Celta de Bigo 9. Antoine Griezmann Atletico Madrid 9.
Kawo yanzu bayan wasa 26 a La Liga, Barcelona ce ta daya a kan teburi da maki 68, sai Real Madrid wadda ta lashe kofin a shekarar data gabata ta biyu mai maki 56 da kuma Atletico Madrid mai maki 51.
Wasannin mako na 27 da za’a ci gaba da buga wa a karshen mako:
Ranar Juma’a 31 ga watan Maris Real Mallorca da Osasuna Ranar Asabar 1 ga watan Afirilu. Girona da Espanyol. Athletic Bilbao da Getafe. Cadiz da Sevilla. Elche da Barcelona. Ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu Celta Bigo da Almeria Real Madrid da Real Balladolid Villarreal da Real Sociedad.
Atletico Madrid da Real Betis Ranar Litinin 3 ga watan Afirilu Balencia da Rayo Ballecano