Mutane da dama sun samu raunuka a ranar Litinin yayin da magoya bayan jam’iyyar PDP da APC suka arangama a garin Fatakwal na Jihar Ribas.
Daya daga cikin wadanda suka jikkata shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, Tonye Cole, wanda ya samu rauni a wuyansa.
- Dubi Ga Sabbin Hanyoyin Kutse A Facebook, WhatsApp Da Asusun Ajiyar Banki
- Farashin Danyen Mai Ya Tashi A Kasuwar Duniya
Tun da farko dai wasu ‘yan jam’iyyar PDP sun yi zanga-zanga a kofar ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ke kan titin Aba a Fatakwal.
Masu zanga-zangar dai sun bukaci duba kayan zaben da dukkanin jam’iyyun siyasa suka yi.
Jam’iyyar APC a karkashin dan takararta na gwamna a ranar Juma’ar da ta gabata ta ce za ta mamaye ofishin INEC a ranar Litinin domin neman a fitar da sahihin sakamakon da aka yi amfani da su wajen zaben gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris domin bai wa jam’iyyar damar shigar da karar a kotun sauraren kararrakin zabe.
Wakilinmu da ke wurin, ya ruwaito cewa yayin da zanga-zangar ta PDP, Cole tare da shugaban jam’iyyar APC na jihar Emeka Beke da wasu jiga-jigan jam’iyyar sun hallara a ttitin Aba, inda suka nufi ofishin INE
Matasan da suka yi zanga-zangar sun garzaya zuwa wajensa, inda suka yi ta jifansa da duwatsu da ledar ruwa.
Nan take jami’an tsaro da ke tare da Cole suka yi masa garkuwa tare da saka shi cikin mota, amma duk da hakan masu zangar-zangar suka ci gaba da jifansa.
Cikin dakika kadan sojojin runduna ta 6 ta sojojin Nijeriya da jami’an ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya da na Sibil Difens suka isa inda suka dinga harbi a iska domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa, daya daga cikin jami’an tsaron da ke aiki da Cole ne ya harbi daya daga cikin masu zanga-zanagr.
Mutumin ya zubar da jini sosai sakamakon harbin da aka yi masa a kafarsa.
Daga baya abokansa sun kai shi asibiti.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, al’amura bas u daidaita a yankin ba.