A yunkurinta na ceto ‘yan kasa daga kangin yunwa da samar da nagartaccen sakamako ta fuskar aikin gona, hukumar kula da share filayan aikin noma ta kasa (NALDA) ta samar da makarantun horaswa ga manoma a jihohin Ogun, Katsina, Abiya da kuma Borno.
Wannan na kunshe cikin wata takarda wadda babban jami’in hukumar NALDA, Kaka Alhaji Mustapha ya rattabawa hannu tare da mika ta ga manema labarai.
Ya ce bayan shirye-shirye daba-daban da hukumar NALDA ke gudanarwa ga manoma mata da maza, yanzu kuma hukumar ta kafa makarantar da za ta rika bai wa su manoman horo a kan dabarun aikin noma, yayin da suma wadanda suka sami horon za su kware domin ganin an kai ga nasara a kan irin ayyukan da ita hukumar ta sanya a gaba.
Haka kuma ya kara da cewa samar da makarantun zai taimaka matuka wajan horas da manoma da kuma gudanar da duk wasu shirye-shirye wanda hukumar take yi cikin sauki, musamman wajan bai wa ‘yan sa- kai da sauran manoma bita a kan aikin gona.
Jami’in ya ce irin ayyukan da hukumar NALDA take aiwatarwa a wasu sassa na kasar, musamman na katafariyar gona mai suna “Integrated Organic Farm Estate” a Jihar Borno suna taimakawa matuka gaya.
A cewarsa, an samar da gonan ne domin kyakkyawan zaton cewa matasa da mata na Jihar Borno za su samu ilimi da dubaru na musamman wajen koyon sana’ar aikin gona, musamman a bangaren harkar kiwon kaji masu kwai da nama, kiwon kifi, kiwon zuma, kiwon dabbobi na shanu da tumaki, koyon aikin sarrafa kayan amfanin gona da kuma sayar da su a kasuwar zamani.
Kaka ya ce makarantun za su gudanar da karatu a mataki na farko, za a fara ne da takardar shaidar difiloma a bangaran fannin aikin gona, sauran kwasa-kwasan sun hada da difiloma ta kimiyyan aikin gona da kiwo (Agricultural Technology & Animal Production) da kuma difiloma a kan kimiyar kiwon lafiya (Diploma in Health Technology).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp