Dan Majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Zariya a Majalisar wakilai ta taraiya Abuja, Honarabul Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa yana daga cikin mutane 15 da suka fi kowa dadewa a Majalisar Dokokin tarayyar Nijeriya wanda kuma ya kasance daga shiyyar Arewa maso yamma.
A wata zantawa da manema labarai a garin Abuja, Hon Tajudeen wanda kuma ya kasance Shugaban Kwamitin a kan Kasa (filaye) da sufuri, ya nunar da cewa a wannan Majalisar karo na goma, zai koma karo na hudu kenan domin ci gaba da ayyukan al’umma a Majalisar.
Ya ce, “a bisa kwarewa na aiki da kuma gudunmuwar dana bayar a Majalisar musamman a kan abin da ya shafi dokoki wanda a yau bamu san gobe ba, babu wani dan Majalisar daya kawo dokoki masu mahimmaci akalla guda 78 kuma yake da dokoki guda 21 wanda shugaban Kasa ya saka musu hannu kamar ni.
“Sannan na dade a Majalisar kusan na shekaru goma sha biyu kuma na rike mukamai daban-daban, kana daidai gwargwado tsakani na da ma’aikatan da kuma abokan aiki sauran yan Majalisar, ina da tarihi mai kyau a wajen su tare da shaidar zaman lafiya da fahimtar juna da zamantakewa.
“Don haka, idan Jam’iyyar mu ta kebe wannan Kujerar izuwa Arewa ta yamma, Kusan babu wanda yake gaba da ni wajen dadewa shi yasa nima nake ganin lokaci ya yi da zan fito domin neman wannan Kujerar ta shugaban Majalisar.
Acewarsa, koda a yanzu Jam’iyyar su ba ta fito ta bayyana matsayarta ba, amma ya zama dole ne sai idan mutum ya fito ya tallata kan sa tare da ra’ayin sa na neman bukatar kamin idan lokacin da Jam’iyyar za ta fito ta bayyana ra’ayin ta tare da su masu ruwa da tsaki da sauran yan Majalisar, toh a lokacin an riga an san da shi don haka zaizo da sauki idan ya kasance shiyyar da yake nema aka ba damar.
“Mun tabbatar da maganar shiyya dole ne saboda a yadda muka samu kanmu a kasar yanzu wanda shugaban Kasa da Mataimakinsa Musulmai ne, Jam’iyyar ba zata yarda ta watsar da damar ba da cewa kowa yaje ya nema domin idan aka yi haka, zai iya kasancewa shugaban Majalisar dattijai ya zama musulmi, shugaban Majalisar Tarayya ya kasance musulmi, don haka na tabbata Jam’iyya za ta so a ce kowace shiyyar an yi musu adalci tare da basu hakkin su.
“Duk wanda kaji yana magana a kan a bude neman ko neman cancanta, yana yi ne bisa son ra’ayin kansa domin idan aka duba a lokacin da aka dawo mulkin damakoradiya a 1999, shugaban Kasa a wancan lokacin ya fito da kudu maso gabas ne, kuma mataimakin sa ya fito daga Arewa masu Gabas ne, don haka idan aka duba yanayin yadda aka raba mukamai a wanchan lokacin, ya yi daidai da irin tunanin mu ne a yanzu.
“Domin Arewa ta yamma wacce ta fi kowace shiyyar yawan Jama’a, sai a ba ta kakakin Majalisar, kudu maso gabas a basu shugaban Majalisar dattawa, haka kudu maso kudu a basu mataimakin kakakin Majalisar, kana Arewa ta tsakiya a bata mataimakin shugaban Majalisar dattawa, shi yasa har yau har gobe shawarar da muke ba Gwamnati kenan da ayi amfani da irin wannan tsari da aka yi amfani da shi a baya saboda shi ne adalci.
“Hakika yin hakan, zai kara takaita korafi a kasar musamman a irin wannan gabar da kawuna sun rarrabu bisa addini da kuma kabilanci saboda yadda aka shigo wannan Zabe a kan muslim muslim tiketi, dole mu yi hattara wajen ganin cewa kowace shiyyar an bata hakkin ta domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.” Inji shi
Da yake martani kan abokan adawar su, Hon. Abbas Tajudeen ya kara da cewa kasancewar takwarorin su sun fi su yawa kuma suna ganin zasu iya kwace wannan Kujerar tun da ba doka ce tace sai wadanda suke da Gwamnati a hannu ne kadai zasu iya zama kan Kujerar ta kakakin Majalisar ko shugaban Majalisar dattijai ba, ya bayyana cewa wannan ya zama kalubale gare su na yadda suka samu kansu a Jam’iyyar APC.
Ya ce, “Dole mu yi hattara domin idan mu yan takarar bamu hada kanmu ba muka tsayar da wanda muke ganin shi ne mafi alheri a gare mu, irin wannan abu da ake fadi mai yuwa ne wanda hakan yasa mu yan takarar mu takwas mukayi taro a gidan kakakin Majalisar inda mu ka yi alkawari a kan kowa Allah Ya ba a cikin mu, sauran zasu hada kai da shi wajen gudanar da harkokin.
Acewarsa, Dan Majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Zariya Hon. Abbas Tajudeen, wannan yana daya daga cikin matakan da suka dauka wajen ganin basu bada dama ga Jam’iyyar adawa sun zo sun yi nasara akan su ba.