A tattauanwarsa da sashin Hausa na gidan radiyon DW, Gwamnan Jihar Zamfara mai barin gado, Bello Mohammed Matawalle, ya yi wata magana mai ban mamaki a kan dalilan da suka sanya ya fadi zaben neman sake mulkin Jihar a karo na biyu, yana ma dora alhakin haka a kan wai taron dangin da sojoji Nijeriya suka yi masa, inda wai suka hada karfi don kayar da shi a zaben da aka yi.
Kayar da Matawalle na daya daga cikin manya-mayan abubunwa bazata da sukia bayar da mamaki a zaben shekarar 2023. Ya sha kayen ne a hannun tsohon ma’aikacin banki wanda ‘yan jam’iyyar APC ke yi wa shaguben cewa, ba kwararren dan siyasa ba ne, wai mutum ne da bashi da kwarewar da zai iya cin zaben ko na karamar hukuma, amma sai gashi mutumin da ke yi wa kallon bashi da kwarewa ya lashe zabe, hukumar zabe INEC ta sanar da shi a matsayin gwamna mai jiran gado a Jihar Zamfara.
Abin da ya faru a Jihar Zamfara, wani taron dangi ne na tsofaffin gwamnoni 3 da manya-manyan ‘yan siyasar jihar masu ji da kansu, suka tararwa sabon dan siyasa da ya shigo fagen siyasa a shekarar 2018, tabbas wannan wani babban lamari ne a siyasance da a halin yanzu ya shiga kudin tarihin siyasar Jihar Zamfara kuma ba za a mance da shi ba a cikin gaggawa.
Matawalle da jam’iyyar APC sun yi duk kokarin da za su iya yi don daburta tsarin zaben, tun daga tayar da hankula a cibiyoyin zabe da kuma kokarin canza alkalumman zaben daga cibiyoyn zabe, mazabu da kanananan hukumomi.
Wannan fa shi ne dai Matawalle da ake zargin ya yin garkuwa da babban jami’in zaben garinsu na karamar hukumar Maradun inda ya nemi ya sake rubuta sakamakon zabe tare da yi masa ariginzon kuri’u, amma godiya ga na’urar BBAS da ‘IRev portal’ da suka sanya aikin da suka yi ya zaman a banza.
Yana da matukar wahala, babban jami’in tsaron jihar da harkokin ‘yan ta’adda suya addabe ta ya fito fili ya mai cewa wai an samar da sojoji 50 don kare kowacce rumfar zabe a fadin jihar. Wannan bayanin kadai ya isa ya karfafa al’umma Jihar Zamfara su yi watsi da Matawalle.
Domin kuwa hakan yana nuna cewa, lallai ya jahilci yadda ake tafiyar da harkokin tsaro a kasar nan, ciki kuwa har da yawan jami’an da ake da su a dukkan bangarorin rundunonin tsaron Nijeriya.
Jihar Zamfara na da kimanin runfunan zabe 3,529. Bamu san inda Gwamna ya koyo darasin lissafinsa ba, amma ko ma wanene ya koya masa lissafi lallai gagarabadau ne, don inda ka lissafa sojoji 50 sau yawan funfunan zabe 3,529, zaka samu 176, 450.
A ta bakin Gwamna Matawalle, kenan an turo sojoji 176, 450 don yin aikin zabe a Jihar Zamfara. Shin mu gaya masa gaskiya ko kuma mu bari gaskiyar ta tayar da shi daga barcin da yake yi? Babban abin da ya rage masa shi ne ya natsu ya mutumta ra’ayin al’ujmmar jihar Zamfara, ya kuma mutunta kansa ta hanyar yin ritaya daga harkokin siyasa ta yadda zai tsira daga abubuwan da za su kunyata shi.
Rundunar sojojin Nijeriya nada dakaru 230, 000, amma abin da Gwamna Matawalle ke kokarin bayyana wa al’umma shi ne dakaru 53,550 cikin sojojin Nijeriya aka tura sauran jihohin Nijeriya don kula da yadda aka yi zaben Gwamna, sauran dakaru 176, 450 kuma aka tura su Jihar Zamfara.
Adaidai wannan lokacin yana da matukar wahala wani mai cikakken hankali ya fahimci hikimar da ke tattare da abin da Matawalle ke kokarin bayyanawa don dukkan maganganunsa sun yi karo da duk wata tunani na hankali da za a iya fahimta. Duk da cewa, a lokutta da dama ya sha nuna yadda baya lissafi da tunani kafin ya furta wasu maganganunsa.
Muna kawar da fuska daga maganganun Gwamnan da ya yi imanin sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki ta APC zai iya bashi nasarar darewa karagar mulki karo na biyu ba tare da wata mastsala ba. Tabbas yana nan yana cikin jimami da mamakin yadda lamarin kayensa ya faru. Duk da haka kuma ba za mu aminta da wasu maganganun da za su nemi jirkita gaskiya ba.
Babu gaskiya a maganganun Matawalle. Ko yaro dan makarantar firamare ba zai aminta da wannan maganganu na sa ba. Gwamnan na nema madafa ne kawai don a tausaya masa. Yana kokarin ya nuna kamar ba wai al’umma jihar suka yi watsi da shi suka kuma yi waje rod da shi ba saboda rashin iya aiki.
Jajirtattun al’umma Jihar Zamfara sun toshe duk wata kofa na magudi, basu samu abin da suka saba yi ba a ranakun zabe.
Tabbas, dinbin matasan Jihar Zamfara wadanda suka gaji da salon mulkin Matawalle suka yi sanadiyyar faduwarsa, ‘yan fanshon da aka kwashe kudaden su na cikin dalilan da suka haifar da faduwar Matawalle.
Banda ma haka, abin nda ya faru da Matawalle lamari ne daga Allah, idan za a iya tunawa, an ji shi a wani faifai bidiyo yana cewa, “In har na ci amanar PDP, kada Allah ya ba ni zaman lafiya har karshen rayuwata, na rantse da Allah. In har zan bar PDP ko in cuci mambobinta, Allah ya tsine mini”.
A takaita surutu Gawmna. Lokaci ne na yin tunani tare da tuba. Lokaci ne na sabon shafi ga Jihar Zamfara.