A halin yanzu dai masu ruwa da tsaki na kokarin ganin an dawo da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), yayin da gwamnatin Tinubu ke shirin karbar mulki.
Sanusi, wanda amini ne ga gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fara samun labaran yiwuwar sake nada shi gwamnan babban bankin.
- Hajjin 2023: Miliyan 3 Kowane Maniyyaci Zai Biya A Bana —NAHCON
- ‘Yan Majalisu Tara Da Ke Zawarcin Kujerar Gbajabiamila
A matsayinsa na wanda ya yi gwamnan CBN tsakanin shekarar 2009 zuwa 2014, Sarki Sanusi ya jagoranci babban bankin kasar nan mai cin gashin ya jagoranci hada-hadar kasuwannin kudi, musamman bayan tabarbarewar tattalin arzikin duniya na shekarar 2008 zuwa 2009.
Bayan haka, darajar Naira ta daidaita daga kusan N155 zuwa $1 na tsawon shekaru hudu.
An ce Tinubu yana son yin sabon tsarin kula da hada-hadar kudi, wanda zai daidaita manufar kasafin kudi don farfado da tattalin arzikin kasar nan da zarar ya karbi mulki ranar 29 ga Mayu.