ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Daure Minista A Uganda Saboda Satar Kwanon Rufi

by Sadiq
3 years ago
Uganda

An daure Ministar gwamnatin Uganda a kurkuku a lamarin da ba a saba gani na rashawa da ya shafi manyan jami’ai, inda ake zarginta da sama da fadi da kwanon rufi da aka tanada don gidajen masu karamin karfi a yankin Karamoja na Arewacin kasar.

An tuhumi Mary Goretti Kitutu, Ministar Kula da Harkokin Karamoja da dan uwanta Michael Naboya Kitutu bisa damfarar gwamnati.

  • Hajjin 2023: Miliyan 3 Kowane Maniyyaci Zai Biya A Bana —NAHCON
  • An Samu Tsohuwar Hedimasta Da Laifin Yi Wa Dalibai Fyade

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Uganda ta bayyana cewa ana tuhumar ‘yan uwan biyu da hada baki a damfarar gwamnati wajen sama da fadi da kayan da aka sayo don amfanin mutane marasa galihu a yankin Karamoja.

ADVERTISEMENT

Sanarwar da hukumar ta fitar ta kara da cewa an tsare ministar a kurkuku har nan da ranar 12 ga Afrilu.

A ranar Alhamis ne dai Minista Mary Goretti Kitutu da dan uwanta suka gurfana a gaban Kotun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Uganda.

LABARAI MASU NASABA

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

An sayo kwanukan rufin don amfani da su wajen gina gidajen masu karamin karfi a yankin Karamoja, yankin da ke fama da rashin ci gaba, kuma yake fama da matsaloli a Arewa Maso Yammacin Uganda kusa da iyakar kasashen Kenya da Sudan ta Kudu.

Wannan abun kunya ya janyo ce-ce-ku-ce da kokawar jama’a da dama a kasar da cin hanci da rashawa suka yi wa gwamnatinta katutu.

Abu ne da ba a saba gani ba na gurfanar da babban mai rike da mukamin siyasa saboda zargin cin hanci da rashawa, kuma Kitutu ce jami’a mafi girman mukami da aka gurfanar a gaban kotu a ‘yan shekarun nan.

Abu mai kama da wannan da ya faru shi ne na 2007, lokacin da aka tuhumi wasu jami’an gwamnati biyu; Jim Muhwezi da Mike Mukula da sama da fadin miliyoyin daloli na bayar da agaji.

Madugun ‘yan adawar Uganda Bobi Wine ya ce tuhumar Kitutu ‘Da walakin ne’, ya kuma zargi gwamnatin Yoweri Museveni da zama mafi muni wajen aikata cin hanci da rashawa.

Mawakin da ya zama dan takarar shugaban kasa ya ce “Kamata ya yi dukkan mambobin gwamnatin Museveni da shi kansa su kasance a cikin kurkuku saboda cin hanci da rashawa”.

Ya kara da cewa “ba za mu yi murnar tuhuma kan kwanon rufi ba a lokacin da ake almabazzaranci da biliyoyin daloli.”

MASU ALAKA

Uganda
Kasashen Ketare

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

August 23, 2026
Uganda
Kasashen Ketare

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

August 23, 2026
Uganda
Kasashen Ketare

Rasha Da Ukraine Sun Zafafa Hare-hare Kan Juna Bayan Yaƙinsu Ya Ɗauki Sabon Salo

August 22, 2026
Next Post
Kakakin Ofishin Jakadancin Sin Dake Amurka Ya Soki Lamirin Ganawar Tsai Ing-wen Da Kakakin Majalissar Wakilan Amurka

Kakakin Ofishin Jakadancin Sin Dake Amurka Ya Soki Lamirin Ganawar Tsai Ing-wen Da Kakakin Majalissar Wakilan Amurka

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.