Shekaru da dama da suka wuce, fannin aikin noma a kasar ya fuskanci kalubale da dama da suka hada da rashin zuba kudi a fannin.
Sai dai, labarin ya canza tun a shekarar 2016 bayan da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta zuba biliyoyin Naira a fanin aikin noma.
- INEC Ta Raba Muhimman Kayyayakin Zabe Don Kammala Zaben Gwamnan Kebbi
- Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Brazil
Gwamnatinsa ta zo da sabbin tsare-tsare da shirye-shirye domin bunkasa aikin naoma da samar da wadacaccen abinci a kasar, musamman domin a Nijeriya ta rage yin dogaro akan shigo da amfanin gona zuwa cikin kasar nan daga ketare, inda hakan ya sa aka samu rage kashe biliyoyin dalar Amurka don shigo da amfanin.
Wasu daga cikin shirye-shiyen da gwamnatin ta kirkiro da su sun hadada, shirin samar da takin zamani na fadar shugaban kasa (PFI), shirin aikin noma na Anchor Borrowers da sauransu.
Sai dai, abin takaici, wasu daga cikin wadannan shirye-shiyen masu kayu, cin hanci da rashawa ya yi masu kakatutu, ko kuma wasu mutanen da ba manoma sun mamaye shirye-shiyen.
Misali shirin aikin noma na Anchor Borrowers gwamnatin Buhari ce ta kirkiro da shi a shekarar 2016, wanda a tun da farko gwmanatin ta kebe Naira biliyan 40, don a tallafawa manoman ta hanyar ba su rancen da bai da kudin ruwa.
Tun a wancan lokacin, sama da Naira tirilyan 1.5 aka rabarwa da manoman a a tsakiyar shekarar 2022 a karkashin shirin.
A cewar rahoton da aka fitar a watan da ya wuce, Asusun bayar da lamuni na dunya IMF, ya dora jimlar kan Naira tiriliyan 1.9 tare da kashi 25 a cikin dari kacal da aka karbo, inda kuma ba a iya karbo Naira tiriliyan 1.4 ba.
Bugu da kari, CBN ta hanyar mukaddashin Darktan sashen samar da bayanai Dakta AbdulMumin Isa ya karyata wannan ikirarin, inda ya jaddada cewa, Bnkin ya karbo kimain kashi 52 a cikn dari na kudin.
Hakazalika, bayan kaddamar da shirin na Anchor Borrowers a 2016, mutane da ba su da wata nasaba da aikin noma, sun ta kafa kungiyoyi kayan masarufi, don kawai su samu rancen kudin na noma.
Misali, a ranar 16 ga watan Maris na 2023, ofishin hukumar EFFC na shiyyar jihar Legas, ta gurfanar da wani mai suna Uche Chigozie Edwin kan damfarar kungiyar masu noman Masara da sarrafa Naira biliyan 1.4.
Har ila yau, akwai kuma zargin badakalar baya da rance Naira biliyan 5.6 na shirin noman Alkama da ke a karkashin kulawa hukumar (NIRSAL), inda hakan ya janyo aka kori wasu ma’aikatan hukumar daga aikinsu.
Bugu da kari, akwai kuma zargin harkalla a shirin samar da takin zamani na fadar shugaban kasa.
Shugaba Buhari ya kadamar da shirin na (PFI) a watan Disambar 2016 bisa yakinin kara karfafa sarrafa takin zamani a cikin kasar nan.
Sai dai, abin takaici cin hanci da rashawa ya bulla a cikin shirin, inda hakan ya haifar da rubuce-rubucen korafi kan zargin wasu jam’ian da ke a cikin shirin kan karkatar da kudaden da aka zuba don samar da takin zamani, da suka kai yawan Naira biliyan 300
Hakan ya tilasta gwamnatin tarayya sake yiwa shirin garambawul.
Kusan shekaru biyu ke nan zuwa yanzu, shirin ya zama tamkar na jeka na yi ka, inda takin zaman ya zamowa maomna kasar nan, musamman kananan manoma tamkar Gwal, ganin cewa farashin Buhu daya ya haura Naira 25,000.
Mafitar akan wannan matslar kamar yadda shugaban manoma na gasakiya na kasa Architect Kabiru Ibrahim, dole ne gwamnati tarayya mai zuwa ta yi dukkan mai yuwa don ganin shirye-shiryen sun ci gaba da daorewa
Ibrahim ya kuma shawarci zababben shugaban kaar mai jiran Gado Boal Tinubu da ya nada minitan aikin gona da raya karkara bisa cancanta wanda kuma ya san yadda daukacin hukomomin aikin noma za su iya gudanar da yyukan su yadda ya kamata.