Sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na musamman da suka shafe kwanaki hudu suna gwabza fada domin samun galaba a kasar, sun amince da tsagaita wuta na tsawon sa’o’i 24.
Tashin hankalin ya kunno kai yayin da fadan da ke ci gaba da yin barazanar jefa kasar cikin rudani.
- Me Ya Sa Dukkan Jami’an Amurka Ke Tattaunawa Kan Kasar Sin A Argentina?
- An Kaddamar Da Bikin Haduwar Matasan Sin Da Afirka Karo Na 7
Miliyoyin ‘yan Sudan da ke babban birnin kasar da sauran manyan biranen kasar, sun fake a gidajensu, inda suka shiga cikin tashin hankali yayin da dakarun biyu suka yi ruwan bama-bamai a wuraren da jama’a ke zama da manyan bindigogi da jiragen sama tare da yin luguden wuta a kan titi.
A ‘yan kwanakin nan mayakan Khartoum suka kai hari kan ayarin motocin ofishin jakadancin Amurka tare da kutsawa gidan wakilin Tarayyar Turai a Sudan, amma babu wani harin da aka kai kan wani jami’i.
A ranar Litinin ne aka kai wa ayarin motocin ofishin jakadancin Amurka hari, kuma rahotannin farko na alakanta maharan da dakarun Rapid Support Forces, kungiyar sa-kai da ke yaki da sojojin Sudan, kamar yadda majiyar ta shaida wa sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.
Ya kara da cewa dukkan mambobin ayarin na cikin koshin lafiya.
Rahotanni sun ruwaito Laftanar Janar Shams El Din Kabbashi, babban kwamandan dakarun kai daukin gaggawa na musamman, yana cewa sojojin za su mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yayin da shugaban rundunar sojin kasar Janar Abdel Fattah Burhan ke cewa dakarunsa za su mutunta yarjejeniyar.
Sai dai dukkanin bangarorin sojin biyu, ba su fito fili su sanar da batun tsagaita wuta nan take ba.
Bayanai sun ce, an sake samun arangama a kusa da hedikwatar sojojin da kuma kusa da filin jirgin sama, wurare biyu masu muhimmanci da ake gwabzawa ke nan yanzu haka, tun bayan barkewar fada a ranar Asabar.
An kuma gwabza fada a kusa da wani muhimmin sansanin sojin sama a Merowe, mai tazarar kilomita 350 daga Arewa Maso Yammacin birnin Khartoum.
Fiye da mutane 185 ne aka kashe yayin da wasu fiye da 1,800 suka jikkata tun bayan barkewar fadan a ranar Asabar, a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya.
Sai dai kungiyar likitocin Sudan ta sanar a ranar Talata cewa akalla fararen hula 144 ne aka kashe tare da jikkata wasu fiye da 1,400.
Adadin wadanda suka mutu zai iya zarce haka saboda fadan da aka yi a birnin Khartoum ya hana kwashe gawarwaki a wasu yankuna.
Wannan lamari dai, ya tayar da hankulan jama’a a wani abu da ake ganin yakin basasa ne, dai-dai lokacin da al’ummar Sudan ke kokarin farfado da tsarin mulki na farar hula ta dimokuradiyya, bayan shekaru da dama suna karkashin mulkin soja.