Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa a cikin shirin namu na girki adon mata.
Abubuwa da Uwargida zata tanada idan zata hada masar dankali:
Dankalin turawa, Attarug, a, Albasa, Maggi da Gishiri, kuri, Mai, Kwai.
Yadda uwargida zaki hada masar dankali:
Zaki samu dankalin turawa mai kyau ki fere shi ki wanke sai ki nika shi ya yi laushi da kauri kada kisaki ruwa a wajan nikan sai idan injin nikan yacije sai ki sa kadan bayan nan sai ki zuba a rubba ki yanka albasa kisaka maggi da gishiri da kuri in kinada dan wani kayan kamshi zaki iya sawa sai kifasa kwan kamar biyu haka sai attaruhun ki wanke shi, ki daka shi ki zuba dai dai yadda kikeso sannan sai ki juya shi so sai kome yaji, sannan ki dora Tandar wato abin suyar masa a wuta sai ki zuba mai kamar cokali biyu idan yayi zafi sai ki dauko kullun nan naki na dankali da kika hadashi da kayan dandano kizuba daidai yadda girman kufin masar yake sai kibarshi sai ta gasu ta yi ja sai ki juya idan kika juya kikaga baiyi ja ba zaki iya maidashi. Amma fa ahankali zakiyi abun dan karya barbaje saboda ba shinkafa ba ce ballan tana yayi karfi bayan nan idan gasan ma ya yi ja kinga ko ina ya yi ja kamar yadda ake masar sai ki kwashe ta. Shikenan uwargida kingama hada masar dankalin turawa aci dadi lafiya
Ana cinta da miyar jajjage
Abubuwan da uwargida zaki tanada:
Mai, Koran tattasai, Albasa, kwai, magi.
Yadda uwargida zaki hada miya jajjage:
Zaki zuba mai a abin soyar ki kiyanka albasa da koran tattasanki sannan sai ki jajjaga attaruhun bayan ki gama shima sai ki zubashi a ciki sai kizuba magi, gishiri idan suka soyu sai ki fasa kwai kamar biyu haka ki zuba a ciki ki rufe ki barshi yayi kamar 30 ko 40 dakika sai ki bude kijuyau amma kada kicika magi da yawa daya ma ya isa sai kici masar ki dashi idan kuma baki da kayan yin miyar jajjage zaki iya ci da yaji.