Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar birni da kewaye, sannan shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai ta kasa, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya roki kotu da ta soke zaben fid-da gwanin da akayi na gwamna a jihar Kano wanda mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna ya samu nasara.
Sha’aban, wanda ya tsaya takara a zaben fid-da gwani na gwamna a karkashin jam’iyyar APC, ya garzaya kotu ne inda yake kalubalantar yadda aka gudanar da zaben, wanda akayi a rufaffen dakin wasa na Sani Abacha dake Kano.
A cikin takardar korafin da dan majalisar ya shigar, ta hannun lauyansa, J.O Asoluka (SAN), a gaban babbar kotun jihar Kano a ranar Alhamis, ya ce zaben Gawuna a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar APC ya sabawa sashi na 84 da karamin sashi na 1,2,8,12 da 13 na dokar zabe wadda aka yiwa kwaskwarima. A cikin kunshin korafin dai, lauyan mai gabatar da kara ya ce abinda akayi a zaben ya sabawa dokokin jam’iyyar APC sannan gwamnatin jihar Kano tayi kutse wajen zaben deliget sannan ta tursasa su wajen zaben wanda take so
Bayan kammala zaben dai an bayyana Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda yayi nasara ya yinda tsohon kwamishinan kana nan hukumomi, Murtala Sule Garo ya zama mataimakinsa.
Sha’aban Sharada dai yana rokon kotu ne da ta soke zaben saboda a cewarsa, zaben yana cike da magudi kuma ya saba da sabuwar dokar zabe ta shekara ta 2022 da aka sanyawa hannu a wannan shekarar.
Har ila yau, sha’aban ya nuna damuwa akan yadda masu mukamin siyasa a cikin gwamnatin jihar Kano suka kada kuri’arsu a zaben na fid-da gwani wanda kuma hakan ya saba da dokar zabe sashi na 84 (13) cikin baka wanda ya hana duk wani mai mukamin siyasa yin zaben fid-da gwani.