Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane uku a wasu hare-hare da suka kai wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Guma da ke jihar Benuwe.
Hakan dai ya zo ne kwanaki uku da kashe mutane biyar da suka hada da wani malamin cocin Katolika da matarsa a kauyukan karamar hukumar Guma.
- Mutum 15 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Sakkwato
- Shugaban PDP Na Shiyyar Kudu Maso Yamma, Adagunodo, Ya Rasu Yana Da Shekaru 62
Mazauna kauyen sun ce harin na baya-bayan ya auku ne da yammacin ranar Litinin a kauyen Tse-Vambe da ke gundumar Mbagwa da kuma yankin Tse-Iortim Torough Mbanyiar, duk a Guma.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa mutane uku ne suka mutu a harin da wasu mahara dauke da makamai suka kai tare da jikkata wasu da dama.
Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na karamar hukumar Guma, Christopher Waku, wanda ya tabbatar wa manema labarai harin a Makurdi, ya ce an kashe mutane uku.
“An kashe mutum daya a Tse Vambe kuma an kashe wasu biyu a yankin Tse Iortim wanda ya zama uku,” in ji shi.
Waku ya nuna damuwarsa kan yadda kusan dukkanin sassan karamar hukumar kwanan nan suka fuskanci kawanya daga wasu mahara dauke da makamai wadanda kuma suka mamaye ko ina da shanunsu.
Ya kara da cewa, “Mun ga su (makiyaya) a ko ina; an kusa kwace garin Guma gaba daya. Mun gansu da yawansu a Yogbo wacce ita ce gundumar Mbayer/Yandev, tun daga Yelwata har zuwa Ukohol, a Ortese da Hirnyam, inda aka kashe mutane a ranar Juma’ar da ta gabata.
“Suna cikin adadinsu a Uvir da Nzorov; karamar hukumar gwamna. A gaskiya ma, a Nzorov, akwai makiyaya da yawa a can da shanunsu, irin su Mbawa, Mbadwem, Mbabai da sauransu.
“Idan mutane suka je gona a yanzu, za su kashe su ne kawai. Suna tilastawa mutane barin gidajensu da tushen rayuwarsu. A makon da ya gabata, Catechist da matarsa suna cikin gidansu lokacin da mahara suka zo suka kashe su. Idan mutane suna kwancr a gidajensu sai kawai su zo su kashe su… wannan aikin dabbanci ne.”
Da aka tuntubi kakakin ‘yansandan jihar Benuwe, SP Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba.