Ana zargin wani mutum mai suna Idris Aminu da ke yankin Ihima Obeiba Ebozohu a karamar hukumar Okehi da ke Jihar Kogi, bisa kashe kishiyar mahaifiyarsa mai suna Salamotu Aminu ta hanyar buga mata karfe.
An ruwaito cewa, Aminu ya hallaka Salamotu ne a daren ranar Asabar a lokacin da ta ke barci.
- Ana Zargin Jami’an Amotekun Da Kashe Matashi Kan 500 A Ondo
- Ba Ni Da Hurumin Gurfanar Da Alhassan Doguwa —Antoni-Janar
Wani ganau ya shaida wa Leadership cewa, kwana uku kafin Aminu ya raba Salamotu da ranta, ya yi kokarin ya hallakata ta hanyar zuba mata guba, amma ta tsallake rijiya da baya.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce, rundunar ta kama wani mai suna Idris Aminu bisa zarginsa da kashe kishiyar mahaifiyarsa ta hanyar kwada mata wani karfe.
A cewarsa, ‘yar mariganyar ce ta ga gawar Salamotu, inda nan take, muka tura jami’inmu suka kamo Aminu wanda a yanzu, yana tsare a hannumu, ana kuma ci gaba yin bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp