Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya bukaci Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC) da ta binciki jami’an fadar shugaban kasa da mambobin hukumar zartarwa ta tarayya (FEC) mai barin gado.
Matawalle ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani ga wata sanarwa da aka ce ta fito daga Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC, yana cewa hukumar EFCC ta aika gayyata ga dukkan gwamnoni da kwamishinoni masu barin gado da nufin fara bincikensu.
Ya ce bai kamata irin wannan binciken ya tsaya kan gwamnoni da kwamishinoni masu barin gado kadai ba, a hada har da wadanda ke aiki a fadar shugaban kasa.
Matawalle ya kuma bukaci shugaban hukumar EFCC da ya tabbatar da cewa bai sanya siyasa a cikin binciken ba, sannan kuma a gurfanar da duk wadanda aka samu da hannu wajen cin hanci da rashawa a gaban kotu.