• English
  • Business News
Wednesday, May 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masu Kwacen Waya 5 Sun Shiga Hannun Jami’an Tsaro A Kano

by Sadiq
2 years ago
in Labarai
0
Masu Kwacen Waya 5 Sun Shiga Hannun Jami’an Tsaro A Kano
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta NSCDC na Jihar Kano sun kama wasu mutane biyar da ake zargin barayin waya ne a Kano.

Kakakin rundunar, Ibrahim Abdullahi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne a ranar Talata a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Fagge a jihar.

  • Jirgin Kamfanin ‘Nigeria Air’ Zai Iso Abuja Ranar Juma’a —Hadi Sirika
  • Kwana 4 Ga Rantsuwa: Yadda Shugabannin Duniya Ke Tururuwar Rantsar Da Tinubu

Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin su ne Faisal Usman mai shekaru 28 da Mansur Isa mai shekaru 38 da Abdullahi Bashir mai shekaru 25 da Ahmed Ibrahim mai shekaru 21 da kuma Zulkifil Bello mai shekaru 25.

Sanarwar ta bayyana cewa, “Sun kasance suna gudanar da ayyukan ta’addanci a kusa da Sabon Gari, cikin karamar hukumar Fagge inda suke kwace wayoyin hannu na mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.”

Kakakin ya bayyana cewa jami’an hukumar leken asiri ne suka gano barayin.

Labarai Masu Nasaba

Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo

‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Sojoji Da ‘Yan Siyasa Wajen Samun Bayanan Sirri – Zulum 

Rundunar, a cewar sanarwar, ta kuma jaddada kudirinta na ci gaba da yaki da ‘yantar da jihar daga duk wani nau’in aikata laifuka.

Ta koka da cewa a baya-bayan nan ana kara samun karuwar matsalar kwace da sace-sacen wayar jama’a a cikin birnin Kano tare da tabbatar da aniyar ta na dakile wannan lamari.

Ya bayyana cewa, a ranar Talata wasu fusatattun mazauna garin suka kone babur mai uku da ake zargin wasu masu kwace waya ke amfani da shi wajen kwace wayar mutane.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BarayiFaggeJami'an TsarokanoKwacen WayaSabon Gari
ShareTweetSendShare
Previous Post

Jirgin Kamfanin ‘Nigeria Air’ Zai Iso Abuja Ranar Juma’a —Hadi Sirika

Next Post

Ma’aikatan Lafiya Sun Tsunduma Yajin Aiki

Related

Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo
Labarai

Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo

46 minutes ago
zulum
Labarai

‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Sojoji Da ‘Yan Siyasa Wajen Samun Bayanan Sirri – Zulum 

3 hours ago
Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho
Ra'ayi Riga

Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho

3 hours ago
Babu Wata Matar Da Aka Gurfanar Saboda Wai Ta Zama Kirista – Gwamnatin Zamfara
Labarai

Babu Wata Matar Da Aka Gurfanar Saboda Wai Ta Zama Kirista – Gwamnatin Zamfara

4 hours ago
Hajjin Bana: Jihar Filato Ta Ba Da Kyautar Kujera 500 Da Tallafin Miliyan 2 Ga Duk Maniyyaci
Manyan Labarai

Hajji: NAHCON Ta Kammala Jigilar Kashi 77 Na Mahajjatan Nijeriya Zuwa Saudiyya 

6 hours ago
Dan Sanda Ya Kashe Abokin Aikinsa Da Almakashi Har Lahira A Kebbi
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Matasa 2 Da Ake Zargi Da Satar Mota A Kebbi

8 hours ago
Next Post
Ma’aikatan Lafiya Sun Tsunduma Yajin Aiki

Ma'aikatan Lafiya Sun Tsunduma Yajin Aiki

LABARAI MASU NASABA

Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo

Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo

May 21, 2025
Za A Gudanar Da Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Karo Na 4 A Birnin Changsha Dake Lardin Hunan

Za A Gudanar Da Baje Kolin Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Karo Na 4 A Birnin Changsha Dake Lardin Hunan

May 21, 2025
zulum

‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Sojoji Da ‘Yan Siyasa Wajen Samun Bayanan Sirri – Zulum 

May 21, 2025
Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho

Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho

May 21, 2025
Babu Wata Matar Da Aka Gurfanar Saboda Wai Ta Zama Kirista – Gwamnatin Zamfara

Babu Wata Matar Da Aka Gurfanar Saboda Wai Ta Zama Kirista – Gwamnatin Zamfara

May 21, 2025
Hajjin Bana: Jihar Filato Ta Ba Da Kyautar Kujera 500 Da Tallafin Miliyan 2 Ga Duk Maniyyaci

Hajji: NAHCON Ta Kammala Jigilar Kashi 77 Na Mahajjatan Nijeriya Zuwa Saudiyya 

May 21, 2025
Dan Sanda Ya Kashe Abokin Aikinsa Da Almakashi Har Lahira A Kebbi

‘Yansanda Sun Kama Matasa 2 Da Ake Zargi Da Satar Mota A Kebbi

May 21, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Na Ƙara Farfaɗowa – Gwamnan CBN

Tattalin Arziƙin Nijeriya Na Ƙara Farfaɗowa – Gwamnan CBN

May 21, 2025
Gwamnan Filato Ya Kafa Kwamiti Don Binciken Hare-Haren Da Ake Kai Wa A Jihar

Gwamnan Filato Ya Kafa Kwamiti Don Binciken Hare-Haren Da Ake Kai Wa A Jihar

May 21, 2025
An Tattauna Hanyar Zamanantar Da Kasa A Dandalin Tattaunawa Na Masanan Sin Da Afirka

An Tattauna Hanyar Zamanantar Da Kasa A Dandalin Tattaunawa Na Masanan Sin Da Afirka

May 21, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.