A bikin mika mulki mai cike da tarihi da ake gudanarwa a Nijeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya fara mika ragamar shugabancin kasar nan ga magajinsa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce ya gama iya kokarinsa sannan ya gamsu da cewa zai mika Nijeriya ga hannun kwararru.
“Na yi aiki mai kyau; Na gama babina. Yanzu lokaci ya yi da wani zai karbi ragamar,” in ji shugaban mai barin gado.
- …Waiwaye Game Da Yadda Aka Rantsar Da Wasu Shugabanni Na Baya
- Ruguntsumin Rantsar Da Sabuwar Gwamnati
Buhari ya yi wannan jawabi ne a lokacin karrama Tinubu, zababben shugaban kasa, a matsayin babban kwamandan gwamnatin tarayya (GCFR), kuma babban kwamandan kasa, kuma zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda aka karrama da lambar yabo ta GCON,” in ji Shugaba Muhammadu Buhari.
Kafin ya bai wa Tinubu da Shettima babban matsayi na biyu mafi girma na kasa, shugaba Buhari ya ce zaben da aka yi wa zababben shugaban kasa da mataimakinsa shi ne ya sanya za a rantsar da su a ranar Litinin 29 ga Mayu, 2023.
Shugaban ya ce, “Ina mika sakon taya murna ga zababben shugaban kasa, bisa nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga Fabrairu, 2023. Jama’ar Nijeriya sun fahimci halayenku na jagoranci, basirar siyasa, da kishinku na yi wa al’ummarmu mai girma hidima, kuma sun dora muku nauyin gudanar da mulkin kasarmu.
“Ba ni da tantama cewa Nijeriya za ta ci gaba da bunkasa tare da samun nasarori a karkashin jagorancinku. Kai ne wanda ya fi kowa hikima a cikin ‘yan takarar da kuka shiga zabe.
“Haka zalika ina mika sakon taya murna ga zababben mataimakin shugaban kasa. Gogewar da kake da shi wajen gudanar da mulki, da jajircewar da ka yi na kyautata rayuwar al’ummar Nijeriya, da kuma jagorancin da ka yi a lokutan kalubale a matsayinka na Gwamnan Jihar Borno, sun sanya ka zama wanda ya cancanta a wannan matsayi. Ina da cikakken kwarin gwiwa cewa za ku yi wa al’ummarmu hidima cikin kwazo da rikon amana.
“Kamar yadda dokar karramawa ta 1963, Laws of Federation of Nigeria, (LFN), ta tanadi karrana Shugabanni Jihohi lambar yabo ta ‘Grand Commander of the Order of the Federal Republic (GCFR)’ yayin da ake bai wa mataimakan shugaban kasa lambar yabo Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Nijariya (GCON).
“A yau, bisa ikon da aka bani, a matsayina na shugaban kasa kuma babban kwamandan rundunar sojojin tarayyar Nijeriya, na bai wa mai girma Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima lambar yabo ta kasa GCFR da ta GCON.
“Yayin da muke murnar wannan gagarumin biki, kada mu manta da gagarumin nauyi da ke tattare da shugabancin. Kalubalen da al’ummarmu ke fuskanta na da muhimmanci, kuma ya zama wajibi shugaban kasa da mataimakinsa su magance su cikin jajircewa da hikima da tausayi.
“Dole ne mu ci gaba da jajircewa wajen bin ka’idojin shugabanci na gari, gaskiya da rikon amana, domin wadannan su ne ginshikin da ci gaban suka dogara.”
Buhari ya bayyana cewa, Tinubu yana da kwarewa da kuma zai iya tafiyar da kasar nan, tare da ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnatinsa.
“Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kana da dogon tarihin hidimta wa jama’a, wanda ke nuna nasarorin da ka samu a fannoni daban-daban. Jagorancin da ka kawo na sauyi a Jihar Legas, inda kuka bar tarihi da ba za a taba mantawa da shi ba a fannonin samar da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, da ci gaban tattalin arziki, wannan ya nuna sadaukar da kai ga rayuwar al’ummar Nijeriya,” in ji shi.
Buhari ya bayyana jin dadinsa ga ‘yan Nijeriya bisa goyon baya da suka ba shi a tsawon wa’adin mulkinsa, inda ya kara da cewa “abin alfahari ne, kuma ina da yakinin cewa Nijeriya na hannun nagartattun mutane.”
Yayin da yake duba wasu kalubalen da ke gaban gwamnatin mai jiran gado, shugaba Buhari ya shawarci Tinubu ya jagoranci kasar nan cikin hikima, jajircewa, da kuma tausayi.
Buhari ya ce gwamnatinsa ta fuskanci kalubale da dama tun farko kuma ta yi aiki tukuru don magance matsalolin.
“Wannan gwamnatin tun daga farko ta fuskanci kalubalen tsaro kamar tada kayar baya, satar mai, garkuwa da mutane da kuma cin hanci da rashawa wanda ya samun gindin zama.
“Tare da manufar siyasa da goyon bayan ’yan Nijeriya da dama, musamman ma rundunar sojanmu, tashe-tashen hankula, ta’addanci, da garkuwa da mutane sun ragu, yayin da ake ci gaba da magance cin hanci da rashawa.
“Duk da kalubalen da na ambata, gwamnatinmu ta samu nasarorin tattalin arziki tsawon shekaru.
Buhari ya bayyana cewa babban nauyin da ya rataya a wuyan hukumomin biyu shi ne tabbatar da cewa duk bayanan da za su taimaka wa sabuwar gwamnati ta fara aiki cikin gaggawa an samar da su ta hanyar da za a iya amfani da su kuma a kan lokaci.
“A yau, ina alfahari da na mika wa Bola Ahmed Tinubu, wasu muhimman takardu guda uku wadanda za su jagorance ka yayin da kake da niyyar ayyana hanyar da gwamnatinka za ta bi.
“Ina fatan za ku samu wadannan takardu domin wannan shi ne karo na farko a tarihin kasar nan da za a samar da cikakkun bayanai na mika wa sabuwar gwamnati.
“Ina ba ku kwarin guiwa da ku kiyaye wannan kuma ku kyautata kwarewar wanda kuka gada a lokacin da za ku bar ofis.
“Har ila yau, yana iya ba ku sha’awar sanin cewa, baya ga wadannan takardu guda uku, ma’aikatu da hukumomi su ma sun shirya takardar mika mulki, kuma a shirye suke su yi wa sabbin shugabannin siyasarsu bayani. Ina son mika godiyata ga sakataren gwamnatin tarayya da tawagarsa bisa wannan gagarumin aiki da suka yi,” in ji shi.
A kan mika mulki ga Asiwaju Tinubu, shugaba Buhari ya ce gwamnati mai jiran gado za ta ci gaba da fafutukar ciyar da mulkin dimokuradiyya da ci gaba.
A nasa bangaren, Tinubu ya yaba wa shugaba Buhari kan tsarin dimokaradiyya, inda ya bayyana cewa ya yi abin da shugabannin baya da suka shude suka yi watsi da su.
Zababben shugaban kasar ya ce Buhari ya kafa tarihi bayan hawansa mulki ta hanyar amincewa da karrama marigayi Cif M.K.O. Abiola da Ambasada Babagana Kingibe a matsayin wadanda suka lashe zaben shugaban kasa na 1993 kuma ya karrama su da lambar girma ta GCFR da GCON kowanensu.
“Kun koma cikin tarihi don daidaita tarihin da aka bata,” in ji shi.
Ya kuma taya shugaban kasar murnar samar da kwakkwaran jagoranci da hangen nesa na tsawon shekaru takwas, yana mai ba da tabbacin cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba idan ya mulki a ranar Litinin.
“Na fahimci girman karramawar da aka min da kuma girman aikin da ke jiranmu,” in ji shi.
Tinubu ya yi alkawarin ba zai bata wa ‘yan Nijeriya da suka amince da shi ba ta hanyar zabarsa a matsayin shugaban kasa.
“Dole ne na gudanar da wannan aiki kuma dole ne na yi shi da kyau. A kan tsaro, tattalin arziki, noma, guraben ayyuka, ilimi, lafiya da wutar lantarki da sauran bangarori dole ne mu tashi tsaye. Jama’a ba su cancanci koma baya ba. Don haka ba zan ba sh kunya ba, ya mai girma shugaban kasa.”
Ya kuma yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa jajircewarsa na samun ci gaba da gudanar da mulkin dimokuradiyya, tare da amincewa da shi a matsayin shugaban da ya dauki matakin jajircewa a lokacin da wasu suka kau da kan su wajen yin abin da ya dace.
Ya kuma mika godiyarsa ta musamman ga shugaba Buhari kan ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokradiyya da kuma karrama MKO Abiola da lambar GCFR, matakin da wasu shugabannin kasar ke tsoron dauka.
Ya ce, “Shugaba Buhari, ka nuna jajircewa wajen daukar tsauraran matakai da wasu suka kasa dauka.
“Daya daga cikin matakan shi ne amincewa da rashin adalcin da aka yi na soke zaben 1993, tare da sanya ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokuradiyya, da kuma bai wa marigayi MKO Abiola babbar lambar girmamawa a kasar nan.”
Zababben shugaban kasar ya kuma nuna jin dadinsa ga shugaba Buhari kan yadda ya karrama shi da mataimakin shugaban kasa Shettima.
“Na gode, mai girma shugaban kasa, da aka karrama mataimakin shugaban kasa, Shettima,” in ji shi.
Asiwaju Tinubu ya kuma mika godiyarsa kan ba shi takardun mika mulki da kuma kwazon aiki da kwamitin mika mulki karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya yi.
“Takardun sun takaita gagarumin aikin da gwamnatinku ta yi. Sun zama tamkar taswira da za su saukaka aiki a gare mu.”