Tsohuwar Hadima ta Musamman ga Gwamnan Kano kuma fitacciyar jarumar Kannywood, Rashida Mai Sa’a ta ce babban burinta ga sabuwar gwamnatin Bola Tinubu shi ne ta tilasta wa magidanta su kara aure.
Rashida ta bayyana burin nata ne a wata hira da ta yi da manema labarai kuma jaridar Aminiya ta rohoto, inda tace, jarumar kuma tana fata gwamnatin za ta dauke musu nauyin kayan aure.
“To mu dai babu abin da muke so Baba Tinubu ya yi mana kamar dauke mana wahalhalun aure da kuma sanya wa duk mai mace daya ya kara, mai biyu ma haka, mai uku kuma ya cike.
“Sannan kuma muna so a ba mu sana’a, wadanda suke da shaidar karatu kuma a ba su aiki.
“Ita ma kuma matar shugaban kasa muna so ta yi koyi da abin da Aisha Buhari ke mana, yadda ta ke debo mu ta saka mu a gaba-gaba”. Inji Rashida Mai Sa’a.