Kasar Iran ta bayyana aniyarta na sake yin hulda da Kasar Saudiyya inda tace “za ta yi maraba da sake dawo da huldar diflomasiyya da Kasar Saudiyya, wadda suka dade ba sa zama a Inuwa Daya”
Kakakin ma’aikatar hulda da kasashen waje ta Iran, Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, inda ya kara da cewa ita ma gwamnatin Saudiyya tana da wannan muradi. Inji BBC Hausa.
Iran da Saudiyya, wadanda su ne manyan kasashe mafiya karfi na Musulmi mabiya Shi’a da Sunnah a Gabas ta Tsakiya, sun katse huldar diflomasiyya a shekarar 2016.
Tun daga shekarar da ta gabata gwamnatocin kasashen biyu sun tattauna sau biyar da nufin sasantawa a tsakaninsu.