Sama da mahalarta bikin aure 106 suka hadu da ajalinsu, sannan an ceto mutum 144 a hadarin kwale-kwale da ya faru a kauyen Egbu da ke cikin karamar hukumar Patigi a Jihar Kwara.
Rundunar ‘yansanda jihar ce ta tabbatar wa Jaridar LEADERSHIP hakan a garin Ilori, babban birnin jihar a ranar Laraba da ta gabata.
- Cire Tallafin Mai: Farashin Kayayyaki Ya Karu Da Kashi 22.41
- Sin: Bai Kamata A Shigar Da Salon Fito-na-fito Cikin Tsarin Ayyukan Hukumomin Hada-hadar Kudi Na Kasa Da Kasa Ba
A cikin sanarwar da rundunar ‘yansandar ta fitar da jami’in hulda da jama’a, Okasanmi Ajayi ya sanya wa hannu ta tabbatar da cewa wadanda suka mutu sun karu zuwa 106 a wannan lamarin.
Sanarwar ta ce kwale-kwalen da lamarin ya rutsa da shi yana dauke da mutane kusan 250 daga kauyen Gboti da ke Jihar Neja, inda zai nufe Patigi a Jihar Kwara lokacin da hatsarin ya faru.
Ta kara da cewa mutanen kauyen Ebu guda 61 suka mutu, sannan mutum 38 daga kauyen Dzakan suka hadu da ajalinsu, yayin da aka samu mutum hudu a kauyen Kpada da kuma wasu uku daga Jihar Kogi, wanda adadin wadanda suka mutu ya kai 106.
“Mun samu nasarar ceto jerin mutum kusan 144,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Rundunar ‘yansandan Jihar Kwara tana sanar da daukacin al’ummar Jihar Kwara cewa mummunan hatsarin kwale-kwale ya afku a karamar hukumar Patigi da ke jihar da misalin karfe 3 na ranar 12 ga watan Yunin 2023. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda na shiyyar Patigi ne ya samu labarin cewa hatsarin kwale-kwale wanda ya afku a gefen kogin Neja.
“Bayan samun lamarin, nan take kwamishanan ‘yansandan Jihar Kwara, ya aike da tawagar ‘yansanda domin su bi sahun sauran ‘yansanda da sauran jama’an tsaron sa-kai na yankin da hatsarin kwale-kwalen ya afku tare da yin aikin ceto.
“An ce jirgin ruwan yana dauke da kimanin mutane 250 daga wani kauye mai suna Gboti da ke Patigi bayan daurin aure zai nufi kauyen Ebu da kauyen Dzakan duk a karamar hukumar Patigi.
“A yayin da aka tashi daga gabar tekun, wani bangare na jirgin da ke gefen injin ya fashe, inda ruwa ya shiga cikin kwale-kwalen, wanda a karshe ya kai ga kifewar jirgin. Duk da kokarin da aka yi na jawo hankalin mutanen kauyen da suka shirya aure na taimakon ceto mutanen da ke cikin jirgin, amma hakan ya citura, inda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 106.
“Daga cikin wadanda suka mutu akwai mutanen kauyen Ebu da suka kai 61, kauyen Dzakan mai 38, kauyen Kpada mai mutum 4 da kuma wasu uku daga Jihar Kogi, wanda adadin wadanda suka mutu ya kai 106 a jimillance, sannan kuma an ceto matane kimanin 144.
“Kwamishanan ‘yansandan Jihar Kwara a madadin rundunar rundunar ‘yansandan jihar ya jajanta wa iyalan wadanda suka mutu, yana mai addu’ar Allah ya jikansu. Ya bai wa ‘yansanda umurnin ci gaba da kokari ceto wadanda lamarin ya rutsa da su tare da samar da tsaro ga wadanda suka jikkata har sai sun murmure da kuma mika su ga iyalansu.”
Ganau daga kauye da lamarin ya faru sun shaida wa manema labarai cewa yawancin wadanda suka mutu sun fito ne daga kauyen Kpada.
Wata ganau mai suna Misis Elizabeth Lad ta bayyana cewa a lokacin da lamarin ya faru an ceto sama da mutum 75 nan take.
Shi ma wani mazaunin Patiga mai suna Malam Isah Gimba ya bayyana cewa an tsamo gawarwaki har guda 15.
Sakataren karamar hukumar Patigi, Malam Idris Pata Mohammed ya ce karamar hukumar ta aike da tawagar masu ceto, domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.
Ya kuma shawarci mutanen kauyen da ke zirga-zirga a kogin Neja da su dunga kulawa da tafiyar dare domin kaucewa kara faruwar lamarin.
Da yake Magana kan lamarin, tsohon shugaban karamar hukumar, Alhaji Usman Ndako ya ce lamarin ya faru ne sakamakon lodi mara misali da aka yi wa kwale-kwalen.
“An makare kwale-kwalen da mutane da kuma kaya kuma kowa ya san cewa a duk shekara sai an samu tsarin jirgi da dare. Domin a shekarar da ta gabata an samu irin wannan lamari cikin dare a kogin.
“Daya daga cikin makarrabaina ya rasa iyalansa guda takwas, yayin da imamin kauyen Pada ya rasa matarsa har guda uku a wannan tsari.” in ji shi.
Idan za a iya tunawa ba wannan ne karo na farko da ake samu hatsarin kwale-kwale a Nijeriya, inda wani ya bayyana cewa a hatsarin kwale-kwale ya ci rayuwa sama da mutum 701 a Nijeriya a tsakanin watanni 34.
Rahoton ya bayyana cewa mutum 701 sun rasa rayukansu a hatsarin kwale-kwale har guda 53 a fadin kasar nan a tsakanin watan Janairun 2020 zuwa Oktoban 2022.
Mutuwar da ta shafi fasinjojin da ma’aikatan kwale-kwalen, an danganta su da wuce gona da iri, tukin ganganci, rashin kula da kwale-kwale da kuma yanayin tashin hankali da dai sauransu.
Binciken ya nuna cewa an fi samun hatsarin kwale-kwale a lokacin damina tsakanin watan Afrilu da Yuli.
Wani rahoto da aka samu ya nuna cewa Jihar Neja ce ta fi kowace jiha yawan samun hatsarin kwale-kwale a kasar nan da mutane 176, sai Kebbi 84 da Anambra mai 80 da Legas mai mutum 72.
Binciken da aka yi a baya ya nuna cewa mutum 233 sun rasa rayukansu a hatsarin kwale-kwale a shekarar 2022, yayin da Benuwai ta samu mutuwar mutane shida, Jigawa 34, Bauchi biyar, Taraba 18; Neja 16, Legas 17, Bayelsa 22, Anambra 77, Delta biyar, Kogi hudu, Sakkwato 29.
A shekarar 2021, an ba da rahoton mutuwar mutane 307 a hatsarin kwale-kwale, inda aka samu mutum 142 a Neja, Kebbi 76, Bayelsa 7, Delta 2, Taraba 5, Sakkwato 13, Kano 40, Jigawa 7, Legas 11 da kuma Ondo 4.
An samu jimillar asarar rayuka 161 a cikin hatsarin kwale-kwale a shekarar 2020. Kebbi ta samu 8, Legas 44, Bayelsa 6, Bauchi 33, Neja 18, Sakkwato 9, Ribas 16, Anambra 3, Delta 10 da kuma Benuai 14.
Wani rahoton ya nuna cewa a cikin shekaru uku da aka yi bitar, Benuwai ta samu mutuwar mutane 20, Jigawa 41, Bauchi 38, Taraba 23, Neja 176, Legas 72, Bayelsa 35, Sakkwato 51, Kebbi 84, Delta 17, Kano 40, Ondo 4, Anambra 80, Kogi 4 da Ribas 16.
A ranar 13 ga Afrilun 2022, akalla matasa 29 ne suka mutu bayan da wani kwale-kwale ya kife a wani kogi a Jihar Sakwato. Yara biyar na daga cikin wadanda suka mutu a hatsarin.
Kwale-kwale da ke dauke da mutane 35 a rafin Shagari ya nutse. Direbobin sun yi nasarar ceton mutane shida.
Haka kuma fasinjoji 15 sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a yankin Ojo da ke Jihar Legas a ranar 8 ga watan Yuli.
Fiye da mutane 50 ne ake fargabar sun mutu bayan kifewar wani kwale-kwale a Jihar Kebbi a ranar 27 ga Mayun 2021, a cewar hukumomi. Akalla akwai fasinjoji 150 ne ke cikin jirgin wadanda akasarinsu ‘yan kasuwa ne.
Kimanin fasinjoji 85 ne ke cikin wani jirgin ruwa daga gadar Onukwu zuwa kasuwar Nkwo Ogbakuba da ke Jihar Anambra a lokacin da ya kife a safiyar wata Juma’a.
Shugaban kwamitin Ambaliyar ruwa na Ogbaru a Anambra, Mista Ogochukwu Nwasike wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce babu wata hukumar gwamnati da ta ziyarci wurin da lamarin ya faru domin ta taimaka wajen gano gawarwakin fasinjojin da suka bata.
Shugabamn hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa Jibril Darda’u ya ce, “A binciken da muka yi, manyan hatsarin kwale-kwale da suka faru a Nijeriya galibi sun fi faruwa da dare kuma yana daga cikin matakan kare lafiyarmu mu daina tafiya da dare. Galibi a bakin kogi, wasu ‘yan kasuwa za su gaya maka cewa a ranakun kasuwarsu za su je su sayar da kayayyakinsu idan sun gama sai su dawo gida ta kwale-kwale da kayan abinci da dabbobi da dare.
“Har ila yau, rashin amfani da riguna na rayuwa yana haifar da asarar rayuka da yawa. Mun sami damar ba da rigunan ceto ne bisa kokarin da muka yi na yin rajistar dukkan jiragen ruwa, domin yana daga cikin hakkin da ya rataya a wuyanmu a yi wa jiragen ruwa rajista.
- Tinubu Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Lamarin
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan hatsarin kwale-kwalen da ya faru a Jihar Kwara, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama. Ya bayar da umurnin a gaggauta gudanar da bincike game da musabbabin hatsarin.
“Na yi matukar bakin ciki da labarin hatsarin kwale-kwalen da ya lakume rayukan al’ummarmu a Jihar Kwara, kasancewar wadanda abin ya shafa baki ne a wajen wani daurin aure.
“Ina jajanta wa iyalai da abokan arziki da wannan mummunan hatsarin ya rutsa da su. Ina kuma jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Kwara bisa afkuwar hatsarin da fatan za a dauki dangana game da wannan hatsari,” in ji Shugaba Tinubu.
Yayin da ya bukaci gwamnatin Jihar Kwara da hukumomin gwamnatin tarayya da abin ya shafa da su duba halin da ake ciki a hatsarin jirgin ruwa.
Shugaba Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta duba kalubalen da ke tattare da tafiya a ruwa cikin kasar nan, domin tabbatar da cewa lamarin tsaro da aiki ya tabbata.
“Ya kamata gwamnatin Jihar Kwara da hukumomin tarayya da abin ya shafa su hada kai don gano musabbabin faruwar wannan mummunan hatsarin da ya faru.
“Ya kamata kuma a ba da agajin gaggawa da taimako ga wadanda suka tsira da rayukansu da iyalan wadanda abin ya shafa,” in ji shugaban Tinubu.