Mataimakin gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnati ta kowa ce, ba tare da la’akari da banbancin siyasa ba.
Gwarzo, wanda ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugaban Jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da sauran Musulmin Jihar murnar bikin babbar sallah, ya jaddada cewa gwamnatinsu za ta kasance mai adalci ga kowa.
- Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano
- Sakon Sallah: Ina Aiki Dare Da Rana Don Ceto Nijeriya -Tinubu
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran sa, Ibrahim Garba Shuaibu ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke gudanar da bukukuwan sallah, lokaci ya yi da za a rika ba da kyauta ta hanyar raba wa marasa galihu da kuma masoyansu.
Ya bukaci al’ummar jihar da su mara wa gwamnatin Gwamna Abba baya.
Gwarzo wanda kuma shi ne kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, ya yi kira ga mabiya Addinin Musulunci da su yi amfani da wannan biki wajen yi wa Nijeriya addu’a, musamman kan tsaro da tattalin arziki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp