Shugaba Bola Tinubu na yin wata ganawar sirri da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; da manyan hafsoshin tsaro a fadar gwamnati da ke Abuja.
Taron na ranar Litinin ya biyo bayan komawar Tinubu Abuja a ranar Lahadi bayan da ya gudanar da bukukuwan Sallah a Legas a makon jiya.
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 7 Da Ceto Wani Mutum A Afganistan
- Me Ya Sa Amurka Ta Sake Komawa UNESCO Bayan Da Ta Sha Ficewa Daga Hukumar?
Ganawar ita ce irinta na farko tun bayan da Shugaba Tinubu ya amince da nadin sabbin hafsoshin tsaro kusan makonni biyu da suka gabata.
An nada su a ranar 19 ga Yuni, 2023.
Mai bai wa shuagaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne ke jagorantar hafsoshin tsaro da kuma mukaddashin Sufeto Janar na ‘yansanda.
Daga cikin wadanda suka hallarci ganawar akwai babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Christopher Musa, babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, shugaban hafsan sojin ruwa, Rear Admiral Emmanuel Ogalla, shugaban hafsan sojin sama Air Vice Marshal Hassan Abubakar da kuma mukaddashin Sufeton’Yansanda, Kayode Egbetokun.
Cikakken bayani na tafe…