Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya bayyana cewar sha’anin ta’addanci da ake fuskanta ya zama babban kalubale ga samar da abinci a kasar nan wanda zai iya zama babban hadari ga rayuwar al’umma.
Babban jigon na jam’iyyar PDP ya bayyana cewar shawo kan kalubalen tsaro zai kawo karcen karancin abinci da jama’a ke fuskanta wanda illarsa ta fi gaban a nanata.
- Ina Son Kara Aure, Ko Me Yake Kawo Matsaloli Tsakanin Kishiyoyi Da Yadda Za A Magance?
- Sojoji Sun Ragargaji Haramtattun Matatun Mai 30 Da Cafke Mutum 42 Cikin Makonni 3 – DHQ
Bafarawa wanda ya bayyana hakan a tattaunawarsa da manema labarai a Sakkwato ya bayyana cewar ya zama wajibi gwamnati ta kara jajircewa wajen inganta sha’anin tsaro ta yadda manoma za su rika zuwa gona ba tare da ko wace irin fargabar kai masu hari ba.
“Kamar yadda muka sani, samar da abinci babban lamari ne a wanzuwar rayuwar mu, abin damuwa ne yadda a halin da ake ciki al’umma ba su iya zuwa gona su noma abin da za a ci. A yanzu haka, mutane da dama a karamar hukuma ta ba za su iya zuwa gona ba, wasu da dama sun gudu daga garuruwan su.”
Kamar yadda ya bayyana ta’addancin da ake fama da shi a yanzu a mafi yawan sassan kasar nan zai zama tamkar wasan yara idan har karancin abinci ya kara ta’azzara don haka ya zama tilas gwamnatin Tarayya ta dauki kwakkwaran matakin shawo kan matsalar.
“Yana da muhimmanci shugabannin kasar nan su sani matsalar tsaro ba wai ta tsaya kawai a ta’addanci ba. Matsalar karancin abinci ta fi muni kan ta’addanci, kuma yanayin zai iya munana idan gwamnatocin jihohi da gwamnatin Tarayya suka sa idanu karancin abinci ya mamaye al’umma.” Ya bayyana.