Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce Sin da Amurka na da bukatar karfafa hadin gwiwa, kuma hakan hanya ce da ta dace kasashen su bi domin kyautata huldar su.
Li Qiang ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, yayin da yake zantawa da sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen a nan birnin Beijing. Yellen dai na ziyarar aiki ta wuni 4 a kasar Sin tun daga ranar Alhamis, ita ce kuma ziyararta ta farko a kasar Sin, tun bayan kama aiki a matsayin sakatariyar baitulmalin Amurka.
Game da tasirin dangantakar kasashen biyu, Li ya ce makomar duniya ta ta’allaka ga yadda Sin da Amurka suka iya kaiwa ga raya dangantakar su. Kaza lika firaministan na Sin ya yi tsokaci game da yadda shugabannin kasashen biyu, suka cimma matsayar fahimtar juna yayin taron Bali da ya gudana a bara, wanda hakan ya share fagen kyautata dangantakar sassan biyu.
Li ya kara da cewa, kamata ya yi Sin da Amurka su karfafa tattaunawa, da lalubo hanyar cimma daidaito kan muhimman batutuwan tattalin arziki tsakanin su, ta yadda za a iya ingiza daidaito, da kyakkyawar makoma ga alakar sassan biyu.
A nata bangare kuwa, Yellen cewa ta yi Amurka ba ta bukatar rabuwa da tsagin Sin, kuma a shirye take ta aiwatar da matakan da shugabannin kasashen biyu suka amincewa a taron Bali, ta yadda za a kai ga bunkasa tattaunawa, da kaucewa rashin fahimtar juna sakamakon sabani, tare da karfafa hadin gwiwa a fannonin habaka daidaiton tattalin arziki, da shawo kan kalubalolin da duniya ke fuskanta, da ba da gudummawa don cimma moriyar juna, a fannin raya tattalin arzikin Amurka da Sin. (Saminu Alhassan)