Akalla mutane 17 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani wajen hakar ma’adanai da ‘yan kasar China suke gudanarwa a Ajata-Aboki a unguwar Gurmana na karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja.
Rahotannin sun ce an kai harin ne da yammacin ranar Laraba inda aka kashe mutane bakwai da suka hada da ‘yan sandan da ke gadin masu hakar ma’adinai da ma’aikata.
- 2023: Bayan Buhari, Dole Dan Kudu Ya Zama Shugaban Kasa – Fayose
- Wata Tawagar ‘Yan PDP Sun Koma APC A Jihar Osun
An ce maharan dauke da muggan makamai, sun isa unguwar ne da misalin karfe 2 na rana, inda suka nufi wajen da ake hakar ma’adinan, sannan suka bude wuta.
Kwamishinan tsaron cikin gida da jin kai na jihar, Emmanuel Umar, ya tabbatar da faruwar harin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, sai dai ya ce kawo yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba.
Ya ce, “Gwamnatin Jihar Neja na son tabbatar da cewa a ranar 29/6/2022 da misalin karfe 2 na rana, bisa ga sanarwar da aka samu cewa ‘yan bindiga sun kai hari a wani wurin hakar ma’adinai da ke kauyen Ajata-Aboki ta gundumar Erena ta karamar hukumar Shiroro.
“An tura tawagar jami’an tsaro zuwa wurin domin kai dauki.”
Umar ya ce yayin da tawagar jami’an tsaro ta hadin gwiwa suka yi artabu da ‘yan bindigar, wanda ya yi sanadin asarar rayuka daga bangarorin biyu.
Ya kara da cewa, “Wani adadin ma’aikatan da ba a tantance ba a wurin hakar ma’adinan da suka hada da wasu ‘yan kasar China hudu an sace su.
“Jami’an tsaro sun hada karfi da karfe domin farautar sauran ‘yan bindigar tare da ceto wadanda suka jikkata ciki har da jami’an tsaro da suka samu raunuka daban-daban an kai su asibitin gwamnati da ke jihar domin yi musu magani.
“Yayin da gwamnatin jihar Neja ke jajantawa shugabannin hukumomin tsaro a jihar da kuma iyalan wadanda aka kashe, gwamnatin jihar ta ba da tabbacin cewa sadaukarwar da suka yi ba zai tafi a banza ba.”
Umar ya ce gwamnatin jihar ta amince da duk kokarin jami’an tsaro na hadin gwiwa da na al’ummomin jihar na ganin an shawo kan matsalar rashin tsaro a wasu sassan jihar.
Sai dai wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa “Kusan mutane 11 da suka hada da ‘yan sanda da mutane bakwai da ke aiki a wurin hakar ma’adinan da farar hula shida ne suka rasa rayukansu a harin.”
Ya ce an kai mutane da dama wadanda suka samu raunuka asibiti kuma suna cikin mawuyacin hali.