Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce, hauhawan farashin kayan abinci a watan Yunin 2023, ya kai kashi 22.79 a cikin dari idan aka kwatanta da na watan Mayun 2023, wanda ya kai kashi 22.41 a cikin dari.Â
Wannan na kunshe a cikin rahoton farashin kayan abinci CPI na wata-wata da NBS ta fitar a yau Litinin.
A cewar rahoton na NBS, karin farashin ya kai kashi 0.38 a cikin dari, inda rahoton ya ce, amma daga shekara zuwa shekara, tashin farashin ya kai kashi 4.19 a cikin dari, idan aka kwatanta da wanda aka samu a watan Yunin 2022 wanda ya kai kashi 18.60 a cikin dari.
NBS ta ce, an samu karuwar farashin ne akan kaya kamar su, man girki, Burodi, hatsi, Dankali, Doya, Kifi, Nama, Kwai, kayan lambu da sauransu.
Sauran kayan da aka samu karin farshin su sune, kudin tsururin matafiya a Jirgin sama, iskar Gas, kayan gyaran ababen hawa, kudin sufurin fasinjoji masu shiga motocin sufuri na haya, kudaden duba lafiyar majinyata, kudaden juyen man mota da sauransu.