Ƙarancin wutar lantarki, sakamakon zafin rana a Zirin Gaza, ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin mazauna yankin tare da haifar da wani gangami a Intanet game da tashar wutar lantarki daya tilo da ake da ita a yankin.
Yanayin zafin ya zarce salsiyas 38 a yankin da ke da iyaka da Tekun Bahar Rum da Isra’ila da kuma Masar, inda mutane sama da miliyan biyu ke rayuwa.
- Barcelona Ta Dauki Oriol Romeu Daga Girona
- Man Fetur Da Ake Sha Ya Ragu Bayan Karin Farashi —NMDPRA
Gaza na samun wutar lantarki kusan megawatt 120 a rana daga Isra’ila, kuma tashar lantarki guda daya ta yankin ce ke samar da karin megawat 60.
Amma hukumomin yankin sun ce Gaza na bukatar kusan megawat 500 a lokacin watannin zafi.
Wasu fusatattun mazauna yankin sun yi korafi a kafofin sada zumunta kan yadda ake ci gaba da katse lantarkin, wanda zai iya kai wa tsawon sa’a 12 a rana, sannan sun yi kira a fara gudanar da aikin ba da wuta ta yadda ya kamata.
Sai dai, sun nuna bacin rai ga Kungiyar Hamas da ke rike da ragamar mulkin yankin, tare da karfafa gwiwar jama’a su fito su daga murya ga mahukunta.