Ministar Muhalli a kasar Ghana, Cecilia Abena Dapaah, ta sauka daga mukaminta sakamakon wani rahoton da aka bankado na samun makudan kudade da suka hada da na kasashen ketare a gidanta, abin da ya sa ta gabatar wa shugaban kasa takardar murabus.Â
Wata jaridar kasar ta ruwaito cewar kudin da aka sace a gidan ministar ya kunshi Dala miliyan guda kudin Amurka da yuro dubu 300 da kuma miliyoyin cedi na Ghana.
- ‘Yan Adawa Ku Zo Mu Yi Aiki Tare A Katsina – Mai Ba Gwamna Shawara
- Mbappe Ya Samu Tayin Fam Miliyan 300 Daga Al Hilal Ta Saudiya
Jama’ar kasar da dama na bayyana damuwa a kan lamarin, sakamakon yadda ake zargin jami’an gwamnatin Nana Akufo-Addo da cin hanci da rashawa.
Shugaba Addo ya nada Dapaah ministan ruwa da muhalli ne lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2017, yayin da ya sake nada ta bayan samun wa’adi na biyu.