Matakin da Gwamnatin Jihar Zamfara ta dauka na bayar da umarni ga al’ummar jihar su fara shirin mallakar makami domin kare kansu daga ‘yan bindiga ya kasance wani babban batu da ake ta sharhi a kai a wannan makon, inda kwararru a bangaren jami’an tsaro da fararen hula ke ta tofa albarkacin bakinsu da tafka mahawara a kan dacewar lamarin ko akasin haka.
Sai dai duk da ce-ce-ku-cen da abin ya haifar, gwamnatin jihar ta nunar da cewa tura ta kai bango a kan rashin tsaron da ake fama da shi a yankunanta, don haka za ta bi duk hanyoyin da doka ta amince da su wajen saukaka wa al’umma irin ukubar da suke sha sakamakon matsalar.
Yadda kashe-kashen al’umma a jihohin Zamfara da Benuwai ke ta kara karuwa a ‘yan watanin nan, ya sanya gwamnatocin jihohin neman hanyoyin dakilewa ko ta wacce hanya. A kan haka gwamnatin Jihar Zamafa ta umarci al’umma jihar su dauki makamai don kare kansu daga ayyukan ‘yan ta’adda.
A wata sanarwar manema labarai, Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa, a shirye take ta jagoranci ganin al’ummar jihar sun mallaki makamai musamman manoma a fadin jihar don kare kansu daga ayyukan ‘yan ta’adda.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Magaji Dosara, ya ce, an umarci rundunar ‘yansandan jihar ta bayar da lasisi ga wadanda suka cancanci daukar bindiga.
Sanarwa ta kuma ce, al’umma za su nemi mallakar makamin ne ta hanun kwamishinan ‘yansandan jihar don kare kansu daga yadda ayyukan ‘yan bindiga ke ta kara karuwa a sassan jihar abin da ya aka yi kaura daga wasu garuruwa, gwamnantin ta shirya samar da lasisin bidigogi 500 don raba wa a masaurata 19 na jihar, ya kuma ce za a samar da wata cibiya ta musamman don tattara bayanai na sirri a kan harkokin ‘yan ta’adda don a samu murkushe su cikin sauki.
Da yake karin haske a kan umarnin daukar makamin don kare kai a wani shirin safe na gidan talabijin na kasa (NTA) da aka gabatar a ranar Larabar nan wanda wakilinmu ya kalla, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Alhaji Ibrahim Dosara, ya nunar da cewa mutanen Jihar Zamfara a shirye suke su kare kansu.
“Gwamnatin Jihar Zamfara ba za ta taba bin hanyar da ta saba wa doka ba. Mun fadakar da jama’a a kan abin da ya kamata su yi. Za mu tafi fadar shugaban kasa mu lallabe shi ya amince mutanenmu su dauki makami su kare kansu… za mu jira mu ga wane irin makami sufeto janar na ‘yansanda zai ba da damar mutane su mallaka, daga nan gwamnatin jiha za ta san hanyar da za ta bi ta taimaka. Ina tabbatar muku da cewa Zamfarawa sun shirya kare kansu ko da karo-karon kudi ne za su yi a tsakaninsu domin su mallaki makamin kare kai, za su yi.” In ji shi.
Ya kara da cewa, sun bi dukkan hanyoyi na doka wajen toshe yadda ake tallafa wa ‘yan ta’adda da makamai, amma wadanda suke cin gajiyar tashin hankalin sun hana ruwa gudu ciki har da bara-gurbi a cikin jami’an tsaro.
“Dukkan ayyukan ta’addancin da ake aiwatarwa jami’an tsaro na da bayanan sirri a kai tun kafin a kai ga aiwatar da su, shi ya sa al’amarin ya kai gwamnati bango, hakan ya sa ta shigar da al’umma cikin yadda za a magance lamarin, don idan akwai makamai a hannun mutane, misali a ce kowane gida akwai, su kansu ‘yan ta’addan za su shiga taitayinsu.” Ya bayyana.
Shi kuwa Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom cewa ya yi, tun da babbar burin ‘yan ta’adda shi ne kashe mutanen jihar don mallakar kasarsu, to lallai al’ummar jihar za su tsayu wajen kare kansu daidai gwargwadon yadda za su iya yi, yana mai cewa, “Kada a dauki shirun da muke yi a matsayin tsoro, in har makiyaya za su iya daukar bindiga AK-7 don kare kansu, sauran al’umma jihar su ma na da ikon kare kansu, don ba za mu yarda wasu baki su kora mu daga kasarmu ta gado ba.
“Mun yi tunanin gwamnatin tarayya da harkokin tsaro ke a hanunta za ta kawo mana dauki amma daga dukkan alamu lamarin ya fi karfinta, don haka mun san matakin da ya kamata mu dauka.” In ji shi.
Sai dai kuma ya yaba wa jami’an tsaro musamman wadanda suka rasa rayukansu a fafatawa da ‘yan ta’adda, duk da kokarin su bai kai ga kawo karshen harkokin ta’addancin ba.
•Filato, Neja Da Imo Sun Yi Hannun Riga Da Zamfara, Kaduna Ta Ki Cewa Uffan
A nasu bangaren, jihohin Filato da Neja da Imo da su ma ke fuskantar matsalar tsaron, sun yi hannun riga da irin matakin da Gwamnatin Zamfara ta dauka, inda suka ce ba za su bi sawu ba, yayin da ita kuma Jihar Kaduna har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto ba ta ce uffan ba.
Kwamishinan Yada labarai na Jihar Filato, Mista Dan Manjang, ya ce, Jihar Zamfara ba za ta zame musu abin koyi ba saboda dalilin matsalar tsaro a jihar ya samo asali ne da yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da kuma sace-sacen al’umma don neman kudi. “Mu namu nau’in matsalar tsaron daban ne.” In ji shi.
A Jihar Neja kuma, Kwamishinan harkokin Cikin Gida, Emmanuel Umar, ya ce, Jihar ba za ta karfafa wa al’ummarta daukar kanana da manyan makamai ba saboda matsalar tsaron da za ta iya haifarwa a yanzu da kuma nan gaba. Ya ce, daga karshe makaman za su bazu ta yadda ba za a san yadda za a yi dasu ba.
Shi ma da yake magana game da jiharsa jim kadan bayan ganawa da Shugaba Buhari, Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma ya ce barazanar tsaron da suke fuskanta a jihar ba ta yi kamarin da za a ce wa mutane su dauki makamin kare kai ba.
•Mahangar Masana Kan Lamarin:
Birgediya Janar Usman Kukasheka (mai ritaya)
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Jami’in tuntuba na Rundunar Soja, Birgediya Janar Usman Kukasheka (mai ritaya) ya ce, yana tsananin tausaya wa al’ummar Jihar Zamfara da ma sassan kasar nan da ayyukan ‘yan ta’adda ya ta’gayyara.
“Ta haka mutum zai fahimci irin matsin lambar da gwamnatin jihar ta Zamfara ke fuskanta. Galibin fargabar da ake yi a kan batun mallakar makamai shi ne kowa zai iya cewa zai bi sahu, kuma ga shi ana fuskantar zaben 2023 wannan babbar barazana ce, da aka ce kowa ya mallaki makami, ta wacce hanya? Akwai dokar mallakar makami, kuma gashi a halin yanzu bindigar AK47 ta kai Naira Miliyan Daya akalla, yanzu inda aka ce kowa ya saya za a iya samun matsala musamman ganin irin matsin tattali arziki da al’umma ke fuskanta.
“Wasu shugabanni sun siyasantar da al’amarin tsaro. Akwai kuma batun ma’adanai na Jihar Zamfara ana haka babu wata cikakkiyar ka’ida kuma babu mai magana, ya kamata a rinka tuntubar masu ruwa da tsaki don samar da mafita, a zauna a duba tsarin da zai yi aiki, akwai lokacin da aka yi wani taron sulhu a garin Mada, tabbas an ga natija da fahimtar juna a tsakanin Fulani da Hausawa. Lallai akwai mafita daga wannan matsalar ba sai an kai ga bayar da izinin mallakar makamai ba.” In ji shi.
Kukasheka ya nunar da cewa, ‘yan ta’adda na amfani da halin talauci da al’umma ke ciki wajen jawo su cikin harkokin ta’addanci, “sai su basu Naira 5,000 su saya musu babur shi kenan su ma sun zama ‘yan ta’adda. Idan aka tafi a kan shirin mallakar makamai, zai kai ga wasu mutane za su rika bayar da bashin kudi ga al’umma su sayi makaman, kuma su yi fito na fito dasu yayin da suka zo karbar kudin bashinsu. Babbar matsalar ita ce yadda tsarin tafiyar da kananan hukumomi ya fadi, gashi tsarin shari’a yana cikin wani halin ni’yasu, mutum zai aikata mugun aiki amma ka gan shi yana yawo ba a hukunta shi ba.
“Idan aka ce a mallaki makamai, to wani irin makamai Kwamishina zai bayar da izinin amfani da shi? To a doka ko IGP ba shi da hurumin bayar da izinin mallakar makamai sai shugaban kasa, don haka wane irin makamai za a bayar da izinin amfani da shi? Ya dai kamata a tattauana sosai da masana kafin a kai ga zartas da al’amarin.” A ta bakinsa.
•Gwamnatin Zamfara Ta Gaji Da Kashe-Kashe A Kullum
– Daggash
Shi kuwa a ra’ayinsa, Tsohon shugaban rundunar sojojin sama, Air Marshal Alamin Musa Daggash (mai ritaya) ya ce, umarnin gwamnati na al’ummar su dauki makamai don kare kai yana faruwa ne don yadda harkokin ‘yan ta’adda na kashe-kashe yake ta karuwa a kullum kuma babu wata alama ta kawo karshensa.
Daggash ya kara da cewa, tsarin dimokradiyyar kasar nan ya ba gwamnan hurumin kare al’ummarsa, ya kamata gwamnatin tarayya ta kalubalance shi in har ba a kan gaskiyarsa yake ba.
“Ina tunanin lamarin ya kai Gwamnan Zamfara bango ne, ka san ta’addancin Jihar Zamfara sai kara karuywa yake yi a kullum, kuma gwamnatin tarayya ta kasa taimaka masa yadda yakamata.” In ji shi.
Tsohon shugaban rundunar sojin saman ya kuma yi tir da tsananin cin hanci da rashawa a kasar nan musamman a bangaren harkokin siyasa.
•A Tsaurara Dokar Mallakar Makami – AIG Felid Ogbaubu
Wani masani a harkokin tsaro, tsohon mataimakin Sufeto Janar na ‘yansanda, Felid Ogbaubu ya ce, gaskiya matsalar tsaro a Jihar Zamfara ta kai inda ta kai, kuma gashi sashi na 14 da 26 na kundin tsarin mulkin Nijeriya ya yi bayani a kan kare rayuwa da dukiyoyin al’umma, lamarin rashin tsaro ya bazu a ko’ina a sassan Nijeriya, shi ya sa yakamata a yi duk abin daya dace don kawo karshensa.
“Shawarata ita ce a aiwatar da matakai na bai daya a sassan kasar nan don Nijeriya na da fadi, a fara da tsaurara dokar kasa a kan mallakar makamai, kamar yadda kasar Saudiya ta yi a kan kwaya, duk wanda aka kama da laifin safarar kwaya hukuncin kisa ake aiwatar masa a can.”
Ya kuma bayyana cewa, “dole mu yi aiki da dukkan tsarin da muke da su a kasa na magance matsalar da ake fuskanta musamman ganin irin yawan rayukan da ake rasawa a kullum, sannan a dakile hanyoyin bazuwar makamai a cikin al’umma tare da zartar da hukuncin kisa ga duk wanda aka tabbatar da laifinsa da masu tuba suna sake komawa harkokin ta’addancin, don rashin hukunta masu laifi yana kara wutar matsalar ce kawai.
“Ya kuma kamata a kara yawan jami’an tsaro a kuma kafa ofishoshinsu a sassa da dama na yankunan karkara, wannan zai taimaka wajen kai dauki yayin da aka samu rahoton aukuwar matsala, sanann a tabbatar da kula da jin dadin ma’aikata tare da biyan kudaden giratuti na wadanda suka rasa rayukansu a yayin fafatarwarsu da ‘yan ta’adda, babbar mafita ita ce a tabbatar da tsaftace al’umma daga dukkan makamai tare da yin komai da aka sa a gaba da gaske babu wasa a ciki saboda daga dukkan alamu Gwamnan Jihar Zamfara ya gaji.” Ya bayyana.
•A Samar Da Kundin Tsarin Yadda Za A Magance Matsalar Zamfara – Dakta Kabir Adamu
Shi ma a nashi bangaren, kwararren masani a kan harkokin tsaro na gida da waje, Dakta Kabir Adamu, cewa ya yi, “a halin yanzu kusan kananan hukumomi da dama na fama da matsanancin mamayar ‘yan bindiga, da farko ya kamata a fahimci irin matakan da gwamnati tarayya ke dauka don kawo karshen matsalar tsaron a Jihar Zamfara, musamman ganin matsalar tsaron ta faro ce daga takaddamar rigima a tsakanin Fulani da Hausawa kuma har yanzu babu wani kundi da aka samar don magance matsalar tsaron a yankin arewa maso yamma. Amma a rikicin arewa maso gabas an samar da kundi da ya samu karbuwa har a wurin kasashen duniya amma a Jihar Zamfara fa babban abin da ke ruruta wutar shi ne rashin gano ‘yan ta’addan tare da hukunta su, wannan ya kai ga ci gaba da karya tattalin arzikin al’ummar yankin gaba daya. In dai ba a yi abin da ya dace ba, to duk wani mataki da za a dauka ba zai kai kawo karshen ayyukan ta’addancin da ake fuskanta ba, mutane za su cigaba da shan wahala ne kawai.”
•Mallaka Wa Al’umma Makamai Na Da Matukar Hatsari —Babban Lauya
Har ila yau a nasa bangaren, Babban Lauyan Nijeriya (SAN), Mista Abdul Balogun, ya ce, dokokinmun sun haramta wa ‘yan kasa daukar makamai ba tare da ka’ida ba.
“Dole sai an samar da doka kafin a iya aiwatar da umanin, in har ka dauki makami ba a kan ka’ida ba doka na iya aiki a kanka a kuma hukunta ka da laifin mallakar makami ba da izini ba,” in ji shi.
Haka kuma wani Lauya, Sylbanus Akpotia, ya amince da ra’ayin takwaransa, yana mai cewa, babban hatsari ne a bar al’umma su dauki makamai ba bisa ka’ida ba don suna iya amfani da shi ba bisa ka’ida ba.
“Al’umma kasar nan masu bin doka da oda ne. Sai an gyara dokokin mallakar makamai kafin a iya aiwatar da irin wannan umarnin, haramun ne mallakar makamai ba tare da izini ba.
“Na fahimci halin da Gwamnan Jihar Zamfara da al’umma jihar ke ciki na ayyukan ta’addanci amma waannan ba hujja ba ce ta karya tanade-tanaden doka”, in ji shi.
•Babu Hikima A Kiran Daukar Makamai Don Kare Kai –Masanin Harkar Tsaro
Wani mai sharhi a kan harkokin tsaro, Manjo Banjo Daniel (mai ritaya), ya ce, babu hikima ko kadan a kiran daukar makamai don kare kai. Ya bukaci Gwmanan Jihar Zamfara ya yi murabus tun da ya kasa sauke nauyin da doka ta dora masa na kare al’ummar jihar.
•Ra’ayoyin Wasu Mutanen Zamfara
LEADERSHIP Hausa ta nemi jin ra’ayoyin mutanen jihar kan wannan lamari da ake tataburza a kai, inda aka samu mabambantan ra’ayoyi.
Tsohon ma’aikacin Jarida a Ma’aikatar yada labarai ta Kasa, Kepas Dogun Taro, ya bayyana ra’ayinsa da cewa, “matakin da Gwamna Matawalle ya dauka na mallakar bindiga don kare kai ya yi dai-dai, sai dai kafin ya ayyana a sanar a kafafen yada labarai ya kamata ya tattauna da Sarakuna da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, sai a sanya hikima wajen ba da umarnin Malakar bindigar don yaki dan zanba ne”, In ji shi.
Shi kuwa Mujitaba Dansadau cewa ya yi, “wannan umarnin mallakar bindiga don kare kai tuni ya kamata a dauke shi don yanzu an makara, mutanen karkara da watsa cikin garuruwa suka yi hijira zuwa wasu garuruwa da mai za su zo su kare kansu bayan an tarwatsa su? Kuma yanzu haka ‘yan bindiga sun mamaye wasu garuruwa suke iko da su tuni kuwa hanyoyi sun zama nasu. Abi nda ya kamata gwamnatin ta fada mana cewa, ta kasa, sai yanzu da ruwa ya kare wa dan kada. Don haka mu yanzu a yankunanmu an san inda ‘yan bindiga suke kamata ya yi gwamnatin ta kai masu hari tunda sun ki bin sulhu wanda an kwashe shekaru uku ana yin sa.” In ji shi
Mujitaba Dansadau ya kara da cewa, “sai dai kuma mallakar bindiga a wannan lokacin yana da ban tsoro saboda lokacin siyasa da zabe ya karato, wasu na iya amfani da su wajen yakar ‘yan adawa ko yi musu sharri, don samun nasarar zabe. Don haka idan gwamnati ta gaza jami’an tsaro ba sa iyawa sai a fito fili a yi mana bayani, amma idan al‘muma suka mallaki bindiga lallai akwai barazanar fiye dana ‘yan bindiga don gida-gida idan suna fada ko matasan anguwa suna fada abu me sauki su yi amfani da bindiga. Don haka gwamnatin ta yi hattara.” Ya bayyana.
•Ina Aka Kwana Kan Irin Wannan Umarni A Jihar Katsina?
Idan ba a manta ba, a watan Disambar bara ne, Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya yi kira ga al’ummar jihar da su nemi makami domin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga da ya mamaye wasu yankuna na jihar ta Katsina
Sai dai wannan kalaman na Gwamna Aminu Bello Masari sun zo da hazo, a ya yin da masana ke ganin kasawar gwamanti a kowane matakin, ita kuwa al’umma na yi wa batun kallon kamar an sakawar godiya linzami ne.
Gwamna Masari dai ya fada a wani taron manema labarai cewa dole mutane su kare kansu tun da jami’an tsaro sun kasa, tare da fadin cewa jami’an tsaron da ake da su sun yi kadan wajan kare rayuka da kuma dukiyoyin jama’a.
“Addinin musulunci ma ya baka damar ka kare kanta daga duk wata barazana da ka iya cutar da kai, a kan haka dole ka kare kanta da iyalanka da dukiyarka, idan har Allah ya dauki rayuwarka a haka, to ana kyautata zaton ka yi shahada” in ji Masari
Haka kuma ya kara da cewa akwai mamaki dan ta’adda ya samu bindiga da zai kawo wa mutumin kirki hari, amma kana mutumin kirki ka kasa samun makamin da za ka kare kanka.
Sannan Gwamna Masari ya yi bayanin matakin da za a bi kafin mallakar bindiga ko makamin da za a kare kai, inda ya ce gwamnati za ta taimaka wajan yin haka hadin gwiwa da rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina domin a kawo karshen wannan hare-hare na ‘yan bindiga a jihar baki daya
Ya kara da cewa akwai tsari da dokokin da za a bi kafin mallakar bindiga wanda jami’an tsaro Jihar Katsina za su bada duk wani bayani da kuma irin bindiga ko makamin da dokar ta bada dama a mallaka.
Babu shakka a lokacin da Gwamna Masari ya yi wannan magana ta yi wa mutane da dama dadi, sai dai masana na ganin akwai sakaci game da bai wa kowa damar mallakar makami domin kare kansa, kuma ka’idojin da aka gindaya na mallakar bindiga ya raunana wannan yunkuri.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa wannan yunkuri na Gwamna Aminu Masari bai samu karbuwa ba a tsakanin dai-daikun jama’a, saboda wancan ka’ida ta mallakar makami, amma dai kungiyoyi irin na ‘yan banga da ‘yan sa kai na ci gaba da rike bindigogi kirar gida.
Haka kuma bincike ya nuna cewa duk wanda ka gani da bindiga ko makami domin kare kansa to mafiyawan su mutane ne da suke zaune cikin daji, amma dai mutanen gari ko mutum na da ita ba zai bari a gani ko a ji labari ba, saboda yadda su kansu hukumomin tsaro ke ganin matakin na Gwamna Masari kamar yana da hatsari a cikin al’umma.