Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke wuta Jamhuriyar Nijar ya karyata labaran kafafen sadarwar zamani da ke cewa an kai hari kan ginin ofishin Jakadancin da ke Niamey tare da banka masa wuta a yayin rikicin mulki da ke cigaba da gudana a kasar.Â
A sanarwar manema labarai da suka fitar a ranar Juma’a dauke da sanya hannun Dakta Liti I. Auwalu, a madadin Ambasada, ya ce, masu zanga-zanga kan rashin jituwar da ke tsakanin jagororin juyin Mulki Nijar da kungiyar ECOWAS sun yi kokarin shiga cikin harabar ofishin Jakadancin a ranar 30 ga watan Yuli, amma jami’an soja da ‘yansanda sun yi gaggawan dakile hakan.
- Masallacin Zariya: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kai 12
- Yadda ‘Hackers’ Ke Amfani Da Hanyar Smishing Wajen Yin Kutse
“A halin da ake ciki, ofishin Jakadancin na nan cikin kulawar sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro. Muna son mu tabbatar bidiyon da ake yadawa karya ne, don haka muna kira ga jama’a da su yi watsi da wadannan bidiyon,” ta shaida.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa ECOWAS a karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, shugaban Nijeriya, ta umarci dakarunta na ko-ta-kwana da su zauna cikin shiri domin afka wa Nijar da yaki domin kwato mulkin demukudiyya daga hannun sojojin Nijar.
Bayan umarnin kuma, sojojin da suka jagoranci juyin Mulkin Nijar sun yi barazanar kashe shugaba Mohamed Bazoum muddin ECOWAS ta yi gigin turo masu soja da zimmar yakarsu.