Ministan tsaro Muhammad Abubakar Badaru, ya umarci jami’an tsaro da su gabatar da jadawali da abubuwan da ake bukata domin kawo karshen kalubalen rashin tsaro a fadin kasar nan.
Kazalika, ya ce, harkar tsaron kasar nan za ta bunkasa a cikin shekara daya.
- Shin Japan Biris Za Ta Yi Da Hakkin Al’ummarta Da Na Makwabtaka?
- Gwamnatin Kaduna Za Ta Raba Tallafi Ga Talakawa Sama Da Miliyan Ɗaya
Badaru ya bayyana hakan ne a shalkwatar ma’aikatar tsaro a yayin da ya kama aiki a matsayin sabon ministan tsaro.
Ya ce, aikinsa da na karamin ministan tsaro da kuma aikin manyan jami’in tsaro, na cikin tsaka mai wuya idan har ba mu iya kawo karshen kalubalen rashin tsaro a cikin shekara daya ba.
A cewarsa, harkar tsaron a zamansa na ministan za ta bunkasa a daukacin fadin kasar nan a cikin shekara daya.
Ya ci gaba da cewa, ba mu da wata hujja ta gazawa a kan nauyin da shugaban kasa ya dora mana, inda ya ce, za mu yi iya kokarinmu wajen tsamo kasar nan daga kalubalen rashin tsaro.
Ya kara da cewa, a matsayinmu na ‘yan siyasa ba za mu jurewa gazawa ba, domin zai yi wuya a ce mun gaza, domin ba za mu yadda da gazawa a wannan lokacin ba.
Bugu da kari, Badaru ya yi alkawarin hada kai da daukacin manyan jami’an tsaro a duk wata, domin a hada karfi da karfe wajen kawo karshen kalubalen rashin a kasar nan.
“Na aminta da daukacin matakan da karamin ministan tsaro ya bayyana, amma a nawa bangaren a yau shi ne za kara jaddada kokarinmu da kuma daukar alkawarin cewa, za mu samar da sauyi a fasalin harkar tsaro na kasar nan.”
Kazalika ya ce, “Zamu kuma bai wa daukacin hukumomin tsaro na kasar nan hadin kai kuma nan ba da jimawa ba, za mu fara gudanar da ganawa da hukumomin tsaro a duk wata bisa nufin lalubo da mafita a kan kalubalen rashin tsaro a kasar nan.”
“Mun yi sa’a shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kansa ya nada manyan jami’an tsaron kuma ya nada mu a matsayin ministocinsa.”
Bugu da kari, ya yi alkawarin yin nazari a kan rahotannin kalubalen rashin tsaro na kasar nan domin a fito da dabarun yadda za a kawo karshen kalubalen rashin tsaro a kasar.
Ya ce, rahotannin na kalubalen rashin tsaron, na nan a ajiye wadanda za su ba mu damar daukar matakan da suka kamata don lalubo da mafita kan matsalar.
A na sa jawabin Hafsan rundunar tsaro Janar Christopher Musa, ya yi alkawarin dawo da zaman lafiya a fadin kasar nan, inda kuma ya yi fatan yaran da ke a kasar nan, za su girma a cikin yanayi na tsaro.