Jiya Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa sun jagoranci taron tattaunawa a tsakanin shugabannin kasashen Sin da Afirka a birnin Johannesburg, inda shugaba Xi ya gabatar da jawabi.
Cikin jawabinsa, Xi Jinping ya ce, kasar Sin na kokarin zamanintar da kanta domin farfado da al’ummar Sinawa baki daya, yayin da kasashen Afirka ke kokarin gina kansu masu zaman lafiya, da hadin kai, da wadata wadanda suke tsayawa a kasa da kafaffunsu. Akwai hanyoyi da dama da za a bi domin zamanintar da kasa, kuma, ya dace jama’ar kasashen Afirka su zabi hanyar da ta fi dacewa domin neman ci gaba. Inganta dunkulewar kasashen Afirka shi ne hanyar da kasashen Afirka da jama’arsu suka zaba domin zamanintar da kasashensu, kasar Sin tana goyon bayan hakan, tana kuma fatan yin hadin gwiwa da kasashen Afirka kan aikin.
Dangane da yadda za a karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da kuma inganta dunkulewar kasashen Afirka, da zamanintar da kasashen a nan gaba, Xi ya ce, kasar Sin na son gabatar da shawarar goyon bayan raya masana’antun Afirka, da aiwatar da shirin taimakawa Afirka wajen zamanintar da aikin gona, da kuma shirin horar da kwararrun Sin da Afirka.
Ya kuma jaddada cewa, a shekarar 2024 mai zuwa, kasar Sin za ta kira taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC, inda za a tattauna neman ci gaba tare. Kuma, kasar Sin da kasashen Afirka za su hada kansu domin raya sha’anin zamanintar da kasa, tabbas, za su samar da makoma mai haske ga al’ummominsu, da inganta dunkulewar dukkanin bil Adama. (Maryam)