Domin karatowar ranar da kotun sauraren korafe-korafen zabe a Kano ta kammala shirye-shiryen yanzu haka kotun ta kammala sauraren kowane bangare tsakanin jam’iyyar NNPP da Gwamna Abba Kabir Yusif ke jagoranta da kuma bangaren jam’iyyar APC mai adawa da Gwamnatin ta Kano, ta gudanar da taron Sallar Alkunut wadda aka gudanar a filin Mahaha da ke kan titin zuwa Jami’ar Bayero da ke Kano.
Gwamnan Abba Kabir Yusif tare da jagoran darikar Kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso na cikin manyan jagororin da suka halarci sallar wadda kwankwasawa daga ko ina cikin birnin Kano suka halarci taron a ranar Asabar.
- Juyin Mulkin Nijar Da Shirin Kai Farmakin ECOWAS Sun Saba Wa Dimokuradiyya
- Xi Jinping: Wajibi Ne A Raya Jihar Xinjiang Yayin Da Ake Kokarin Zamanintar Da Kasa
An bayyana babban dalilin shirya wannan sallar kamar limamin da ya jagoranci sallar ya bayyana inda ya ce makasudin shirya wannan taron addu’a shi ne domin neman amincewar Allah don samun nasarar shari’ar da ake kan zaben da ya tabbatar da Abba Kabir Yusif a matsayin Gwamnan Kano.
Ya ce ya zama wajibi jama’a su tuna irin ayyukan alheri da ke cikin wannan gwamnati wanda hakan ya sa dole a dage da addu’a musaman don ganin yadda wasu makiyan ci gaban Kano ke kokarin kulla wata kiturmura domin haramtawa Kanawa ci gaba amfanar alheran wannan Gwamnati.
Da ta ke jarin haske jim kadan da kammala Sallar Alkunutun, mashawarci na musamman kan harkokin addinai na II, Gwani Musa Hamza Falaki ya bayyana cewa masoya kishin ci gaban Jihar Kano ne suka shirya wannan taron addu’ar, saboda sai ya kara tabbatarwa da Gwamna tabbacin Alarammomi na cI gaba da yi wa wannan addu’o’in samun nasarar da ake fata.
Daga nan sai Gwani Musa Falaki ya mika godiyarsa ga wadanda suka gudanar da addu’o’in.