ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharuda 5 Da Tinubu Ya Gindaya Wa Ministocinsa

by Sadiq
2 years ago
Tinubu

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya umarci sabbin ministocinsa su zage damtse don kawo sauye-sauye masu kyau ga rayuwar ‘yan kasar nan.

Ya bayar da umarnin ne yayin taron majalisar zartarwarsa ta farko da ya jagoranta a ranar Litinin a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

  • Za Mu Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci -Kwamitin Rabon Abinci A Adamawa
  • Har Yanzu Jakadan Faransa Bai Fice Daga Jamhuriyar Nijar Ba – Macron

Taron ya mayar da hankali kan cimma muradan gwamnatin Tinubu don samar da hanyoyin ci gaban tattalin arziki da wadata al’ummar Nijeriya da kuma kawo karshen talauci tare da jaddada muhimman ayyukan da ke gaban gwamnati.

ADVERTISEMENT

Ga muhimman sharuda biyar da shugaban ya zayyana:

1. Ba za a lamunci rashin kwazo ba: Shugaba Tinubu ya kafa wani tsari da zai sa ido wajen tabbatar da rikon amana da kuma tantance ayyukan da suka rataya a kan kowane minista.

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Ya ce ba zai lamunci rashin kwazo daga wurin ministocin ba.

2. Sabon Tsarin Tattalin Arziki: Shugaban ya yi kira kan samar da sabbin dabarun bunkasa kasafin kudi na cikin gida da za su mayar da hankali wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya. ”

Gwamnatin ta himmatu wajen sake farfado da harkokin kudadenmu na gida don walwalar ‘yan Nijeriya,” a cewar Tinubu.

3. Ayyuka ba yawan lokacin mulki ba: Shugaba Tinubu ya jaddada cewa mukaman na ministocin ba nadi ne “yi-aiki-a-biya-ka” ba amma yana mai cewa ana auna mutuncin minista ne bisa irin ayyukan da ya yi wa kasa.

4. Dabarun samar da tsaro da ci gaban kasa: A kalaman shugaban, majalisar tana da alhakin aiwatar da manufofin da za su “gyara tattalin arzikin kasa tare da tabbatar da ci gaban hadin kai da kuma karfafa tsaro don samar da zaman lafiya da wadata a Nijeriya.”

5. Jagoranci mai sauki da karbar shawarwari: Shugaba Tinubu ya ce ya bude duk wata kofa ta karbar shawarwari don ciyar da gwamnatinsa gaba, yana mai tabbatar da cewa “a shirye nake na ba da hadin kai tare da sauraren jama’a.”

Shugaban dai ya gargade ministocin da su yi kokari tare da ba da himma wajen cimma kashin farko na ajandar da gwamnatinsa ta sa a gaba guda takwas cikin shekaru uku da ke tafe.

Ya kuma bukaci su yi aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin kasar saboda Nijeriya na cikin mawuyacin hali.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Next Post
Zargin Bi-ta-da-ƙulli:   An Hana Kotun Ɗa’ar Ma’aikata Da EFCC Da ICPC Ci Gaba Da Binciken Shugaban Yaƙi Da Rashawa Na Kano

Zargin Bi-ta-da-ƙulli: An Hana Kotun Ɗa'ar Ma'aikata Da EFCC Da ICPC Ci Gaba Da Binciken Shugaban Yaƙi Da Rashawa Na Kano

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.