Biyo bayan kifar da gwamnatin kasar Gabon da manyan sojin kasar suka yi a jiya Laraba, wasu daga cikin shugabannin da ke a Nahiyar Afirka, don su ci gaba da zama a madafun ikonsu, sun fara yi wa manyan jami’an sojin kasarsu ritayar karfi da yaji.
Misali, shugaban kasar Rwanda kuma babban kwadan askarawan kasar Paul Kagame, a jiya Laraba ne, ya amince da yi wa Janar-Janar na soji 12 da kuma wasu dubban manyan soji ritaya.
- Mutum 900 Kacal Aka Gano Cikin 15,000 Da Suka Bace A Arewa Maso Gabas – ICRC
- Matsalar Tsaro: ‘Yan Nijeriya 23,000 Sun Yi Batan-dabo – Gwamnatin Tarayya
A cikin wata sanarwar da rundunar tsaro ta kasar ta fitar, ta ce Kagame ya amince da a yi wa manyan soji guda 83 da kananan soji shida da kuma wasu manyan soji guda 86 wadanda ba a riga an kaddamar da su ba da kuma adadin wasu guda 678 da kuma kwararrun aikin kiwon lafiya guda 160.
Wasu daga cikin wadanda aka yi wa ritayar ta karfi da yaji sun hadar da Janar James Kabarebe, Fred Ibingira Laftanar Janar na biyu Charles Kayonga, da Frank Mushyo Kamanzi.
Kagame ya kuma amince da yi wa Majo-Janar Martin Nzaramba, Manjo-Janar Eric Murokore, Manjo-Janar Augustin TuraAbba, Manjo-Janar Charles Karamba da kuma Manjo-Janar Albert Murasira ritaya.