Bullar cutar kyandar biri a kwanan nan a wasu kasashen Turai da Amurka ta yi matukar jawo hankalin jama‘a. Sai dai wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma sun sha yin amfani da hotunan ‘yan Afirka da suka harbu da cutar a lokacin da suke ba da rahoton bullar cutar, duk da cewa hukumar lafiya ta duniya WHO ta sha jaddada cewa, akasarin wadanda suka harbu da cutar a kasashen Turai da Amurka ba su taba zuwa Afirka ba.
A game da wannan, kungiyar ‘yan jaridar waje a Afirka (FPPA) ta fitar da sanarwa, inda ta bayyana rashin jin dadinta cewa, hakan zai taimaka ga nuna bambanci ga al’ummar Afirka tare da dora musu laifin cutar.
Ta kuma kara da cewa, “Ko kafofin na neman kare tsabtar fararen fata ta hanyar shafa wa bakaken fata bakin fenti.” Wani mai bibbiyar shafin twitter ma ya ce, “idan ka duba hotunan, za ka yi zaton a Afirka ne cutar ta bulla, sabo da yadda kafofin yada labarai na kasashen yamma suka nuna hotunan hannayen ‘yan Afirka a rahoton. Amma da ka karanta bayanin, za ka gane cewa, ba shi da nasaba da Afirka.”
Wannan ya sa mu tunawa da yadda kafofin yada labarai na kasashen yamma suka yi ta kokarin siyasantar da cutar Covid-19 a farkon barkewarta, don neman shafa wa kasar Sin bakin fenti.
WHO ta sha jaddada cewa, cuta ba ta san kasa ba, domin tana iya bulla a ko’ina a duniyarmu, tare da haifar da tasiri ga al’ummomi duk kabilunsu da launin fatansu da kuma arzikinsu.
Idan har ana maganar kwayoyin cuta, babu abin da fararen fata suka fi sauran al’umma da shi. Cuta abokin gaban ‘yan Adam ce, don haka, a duk lokacin da cuta ta bulla, kamata ya yi ‘yan Adam su hada kansu, a maimakon neman shafawa wasu bakin fenti.(Mai zane: Mustapha Bulama)