A yau Laraba 6 ga wata ne aka rufe bikin baje kolin cinikayyar ba da hidima na kasa da kasa na kasar Sin (CIFTIS) na shekarar 2023 da aka shafe kwanaki biyar ana yinsa. Ya zuwa tsakar ranar, mutane kusan 280,000 ne suka halarci bikin na bana, inda suka cimma nasarori sama da 1,100, wanda ya kara inganta halarcin mahalarta kasashe daban daban, tare da kara yin tasiri a duniya.
A yayin da take amsa tambayoyi game da CIFTIS a gun taron manema labarai da aka saba gudanarwa a wannan rana, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin ta dauki nauyin baje kolin cinikayyar ba da hidima ne da nufin raba damar samun bunkasuwa ta fuskar cinikayya tare da bangarori daban daban, da ba da sabbin gudummawa wajen inganta mu’amalar cinikayya a duniya, da kara azama wajen sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya.
Jami’ar ta kara bayyana cewa, tattalin arzikin duniya yana bunkasa idan an bude, kuma yana raguwa idan an rufe shi. Kasar Sin tana son yin aiki tare da dukkan bangarori, wajen sa kaimi ga bunkasuwar hadin gwiwa ta hanyar bude kofa ga kasashen waje, da kiyaye cinikayya cikin ‘yanci, da tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, da samar da karin hidimar kasar Sin ga duniya baki daya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)