Gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar Katsina sun jinjinawa ƙoƙarin gwamna Dikko Umar Raɗɗa bisa amincewa da ɗaukar malaman firamare da sakandare kimanin 7,325.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwar da shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula da sakatarensa a jihar Katsina, Abdulrahaman Abdullahi Dutsinma da Tukur Suke Tama suka sanya wa hannu aka rabawa manema labarai a Katsina.
- Har Yanzu Dokar Ababen Hawa Na Aiki A Katsina —Gwamnatin Jihar
- Ba Zan yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba, Cewar Dikko Radda
Sanarwar ta ce wannan abin a raba ne ganin yadda gwamnati ta ɗauki malaman wucin gadi na S-Power da kuma ‘yan sakai na makarantun sakandare a matsayin malamai na dindindin.
“Ya zama wajibi gare mu da mu jinjinawa gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Raɗɗa saboda wannan yunkuri irin sa na farko a tarihin Katsina, wanda muke da tabbacin hakan zai sauya yanayi da tsarin koyo da koyarwa a jihar baƙi ɗaya” inji shi.
Haka kuma gamayyar kungiyoyin farar hula ta nuna godiyarsa ga kwamitin da ya shirya jarabawar ɗaukar Malaman ba tare da yin wani katsalandan ba, wanda hakan ya tabbatar da ingancin aikin da kwamitin ya yi tunda babu korafe-korafe
Kazalika sanarwar ta ce, wani abu mai matuƙar mahimmanci akan wannan lamari shi ne, yadda aka amince da duk shawarwarin da kwamitin ya bada ga gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa tare da neman amincewar nada horo ga duk sabbin malaman da aka ɗauka.
Daga ƙarshe dai gamayyar kungiyoyin farar hula ta yaba da wannan kokari tare da yin kira ga gwamna Dikko Raɗɗa ya duba halin da ma’aikatan wucin gadi da ke ɓangaren hukumomin kiwon lafiya a fadin jihar Katsina.