Gwamnatin Kano ta kori kwamishinan kasa da tsare-tsare na jihar, Adamu Aliyu Kibiya da kuma mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin matasa Yusuf Imam da aka fi sani da ‘Ogan Boye’.
Kwamishinan yada labarai na Jihar, Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana wannan mataki a ranar Juma’a a wata gana wa da ya yi da manema labarai.
Dantiye ya kuma gargadi dukkan masu rike da mukaman gwamnati da su iya bakin su daga kalamai marasa kan gado.
An sauke jami‘an ne bisa zargin furta wasu kalamai na yin barazana ga Alkalan da suke shari‘ar kararrakin zaben Gwamnan jihar.
Kwamishinan ya kuma yi Allah wadai da kalaman hadiman biyu na yin barazana wa alkalan, ya ce, dukkaninsu ba su yi maganar a madadin gwamnatin jihar ba illa son zuciyarsu.
“Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya na matukar mutunta sashin shari’a da dukkanin jami’an sashin shari’a balle ma alkakai.” Inji sanarwar