A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano ta dauki rukunin farko na daliban sakandare 158 zuwa jihohi biyar a karkashin shirin musayar dalibai.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi, Balarabe Kiru, ya fitar ranar Lahadi a Kano.
- Abba Gida-Gida Ya Dakatar Da MD Na KASCO Kan Zargin Badakalar Hatsi
- Da Dumi-dumi: Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar Da Abba Gida-gida Ya Shigar A Gabanta
Kiru ya ce a ranar 19 ga watan Agusta ma’aikatar ta gudanar da jarrabawa tare da tantance daliban da za su Makarantun Musanya a Jihohin Arewa 19 na Tarayyar Nijeriya da Kwalejin Bilingual da ke Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Kiru ya ce an kai kashin farko na wadanda suka yi nasara da wasu dalibai zuwa jihohin Katsina, Borno, Benue, Jigawa da Kebbi.
Sanarwar ta ce, a ranar 20 ga watan Satumba ne ake sa ran za a kai kashi na biyu na daliban da ke karkashin shirin zuwa sauran jihohin Arewa.
Gwamnatin mai ci ta Gwamna Abba Yusuf ta bayar da duk wani tallafi da ake bukata domin ganin an samu nasarar shirin.
Sanarwar ta yaba da yadda iyaye ke ba ma’aikatar hadin kai a kokarinta na ganin shirin ya kara bunkasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp