Wasu ‘yan fashi da makami sun yi wa wani mai daukar hoto na jaridar PUNCH, Elliot Obadje fashi a karkashin gadar masu tafiya a kafa da ke unguwar Mile 12 Jihar Legas a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida daga wani aiki.
Obadje ya bayyana cewa, ya je Kosofe da ke Ketu ne domin daukar wasu hotunan ginin da ya ruguje, yayin da wasu mutane biyu suka yi masa fashi, inda suka yi masa fashin kudin da ya ciro daga wata na’ura mai sarrafa kanta.
- Kisan Mummuken Cutar Mashako A Nijeriya Da Sassan Duniya
- Kisan Mummuken Cutar Mashako A Nijeriya Da Sassan Duniya
Obadje ya ce, “Bayan na kammala aikin daukar hoton ginin da ya ruguje, sai na tsallaka titin zuwa daya bangaren domin in ciro wasu kudi daga ATM din saboda ba ni da isassun kudin da za su kai ni gida. Amma nan da nan na bar rumfar ATM, wasu mutane biyu suka tare ni da wuka, suka yi min fashin kudin da na ciro yanzu.”
Ya kuma bayyana cewa bayan faruwar lamarin da misalin karfe 6:50 na yamma ya je ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yansanda na Mile 12, kuma nan take ‘yansanda suka bi shi zuwa inda lamarin ya faru.
Ibrahim also stated that the Mile 12 police station would transfer the case to the Ketu Dibision of the Nigeria Police where the suspect would be charged to court after the conclusion of the inbestigation.
Da yake bayyana cewa ‘yansandan sun samu nasarar cafke daya daga cikin mutanen da suka yi masa fashi ne kawai.
Da aka tuntubi jami’in ‘yansandan bincike Amos Ibrahim ya shaida wa manema labarai cewa ya kama wanda ake zargin dan fashi da makami mai suna Ayinde Opeyemi Amoo, bayan wanda aka yi fashin ya gano shi.
Ibrahim ya kuma bayyana cewa ofishin ‘yansanda na Mile 12 zai mika karar zuwa sashen Ketu na rundunar ‘yansandan Nijeriya inda za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan kammala bincike.