Zawiyyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group reshen Jihar Sakkwato ta shirya gagarumin Maulidin Annabi Muhammad (SAW) domin murnar zagayowar lokacin haihuwarsa, inda al’ummar Musulmi daga sassan Nijeriya har ma da kasashe makota suka halarta.
Maulidin wanda ya gudana a Babban Zauren Taro na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Umaru Aliyu Shinkafi da ke Sakkwato, na bana shi ne karo na uku da Zawiyyar take shiryawa a Sakkwato.
Daga cikin abubuwan da suka gudana a maulidin akwai karatun Alkur’ani mai girma, da littafin Tahni’a da na Lamiyya sai karanta tarihi da yabon Annabi (SAW) wanda Shehu Ibrahim Inyass ya rubuta.
Har ila yau, an mike tsaye tare da yin shiru na tsawon minti daya domin jinjinawa da addu’a ga Falasdinawa da ke yakin kwatar ‘yanci da Yahudawan Isra’ila.
Da yake gabatar da karatun maulidin, babban malamin da ya jagoranci maulidin, Sheikh Isma’ila Umar Almaddah wanda ya karanta wata mukalar da Shehu Ibrahim Inyass ya rubuta a shekarar 1962 tare da fassarawa daga larabci, ya bayyana cewa, “Allah ya yi mana baiwa da Manzon Allah (SAW), baiwar da ta game ko ina da ina har Manzon Allah ya kai karshen zama shiriya da wayewa.”
- Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Gudanar Da Maulidin Manzon Allah (SAW) Na Bana
- Kyawawan Abubuwa Da Allah Ya Yi Wa Manzon Allah (SAW) Na Girmamawa
Ya kuma yi bitar yadda wayewa ta faro tun daga kan Annabi Adamu (AS) har zuwa zamanin da muke ciki musamman ta fuskar ‘yantar da Dan’adam daga yankawa zuwa yanka dabbobin ni’ima, da sana’o’i da sauransu.
Sheikh Isma’ila Mai Diwani ya kuma yi kira ga malamai da dukkan al’ummar musulmi kowa ya rika fadada ilimi da zurfafa bincike da fahimtar Alkur’ani mai girma da sauran ilimomin Addinin Musulunci domin kara fahimtar ci gaban da ake samu na zamani.
Ya kara da cewa, duk ci gaban da ake samu a bangaren kimiyya da fasaha ba bakon abu ba ne, musulunci ya tattara komai, muna da su a Alkur’ani, “don haka ne ma Alkur’ani ya yi daidai da kowane zamani. Muna kira ga duk musulmi mu rika fassara ilimominmu na musulunci da abubuwa na zamaninmu. Abubuwan da aka fassara da su na baya kamar hukunce-hukuncen bayi suna nan a bar su don ilimi amma kuma mu fadada fahimtarmu ta addini kan abubuwa na zamaninmu.
“A yau an wayi gari, idan muka ga wani abu an kera na ci gaba, babban abin da muke fara tambaya shi ne halal da haram. Ba za mu yi tunanin yaya aka kera wannan ba. Abubuwa na halal da haram Allah ya fitar mana da su a fili baro-baro, amma yau an shigar da su ko ina da inda ya kamata da inda bai kamata ba. Wannan sai ya takure fahimtarmu a kan abubuwa na kimiyya da fasaha na zamani da ake ci gaba da yin su a wannan zamanin. Lallai har abada idan ba mu sauya wannan dabi’a ba, musulmi ba za mu taba samun ci gaba wajen kere-kere da fasahohi na zamani ba.”
Dangane da yakin da ake yi tsakanin Falasdinawa da Yahudun Isra’ila kuwa, Sheikh Isma’ila Umar Almaddah ya yi kira ga dukkan al’umma Musulmi su taimaki Falasdinawa da addu’a.
“Mu taya su addu’a Allah ya taimake su ya karya Yahudawa da ke zaluntar su bisa taimakon Amurka. A yau kowa yana da ‘yanci a duniya amma ban da Falasdinawa. Allah ya karya Isra’ila tare da mai taimakonta Amurka. Saboda zaluncin Amurka Shehu Ibrahim Inyass (RA) a matsayinsa na Shehul Islam ya taka kusan ko ina amma ar mutuwa ta zo masa bai je Amurka ba, kusan babu inda bai je ba a duniya har Beijing na Kasar Sin, da Hong Kong da Bangkok. Amurka Papalolo ce, babu kasar da ta kai ta yawan cin bashi a duniya amma ita ce gaba-gaba wajen taimakon zaluncin Isra’ila. Allah ya taimaki Falasdinawa ya ba su nasara su samu ‘yancin kansu.”
Har ila yau da yake amsa tambayoyin manema labarai, Sheikh Isma’ila Mai Diwani ya ce, “Allah ya hada mu da samarin wannan gari mai albarka a karkashin Addinin Musulunci da Darika da Failar Shehu Ibrahim (RTA), muke taimakekeniya a tsakaninmu cikin son Allah da son Manzon Allah (SAW) da son Bayin Allah Waliyyai. Muna rokon Allah ya kawo mana ci gaba a kasarmu, rayuwarmu ta yi kyau a duniya, rayuwarmu ta yi kyau a lahira in sha Allahu.
“Bayan haka, manufar Maulidi a Musulunci ita ce murna da kyautar da Allah ya yi mana. Ubangiji Tabaraka wa Ta’ala ya umarci Annabi Musa (AS) a bakin Annabinmu (SAW) a bakin Alukr’ani ya tunatar da mu kwanakin Allah (wa zakkirhum bi ayyamillah). Allah ya ce ya tunatar da mu kwanakin Allah, ma’anar kwanakin Allah kamar yadda malamanmu suka fassara mana, ana nufin ni’imomin Allah (ayadillah). Kwana duk iri daya ne, jiya da yau da gobe duk daya ne, amma abin da yake faruwa a cikinsu shi yake bambance su. To abubuwan da suka faru a cikin kwanan su Allah yake so a tunatar da mu…
“Akwai abubuwa da yawa na ni’omin Allah da suka faru a kwanaki. Akwai murnar abubuwa da yawa, akwai ran da Annabi (SAW) yake murnar an canja masa alkibla, duk wadannan kwanaki ba don an haifi Manzon Allah (SAW) ba za a same su? Ashe ran da aka haifi Manzon Allah (SAW) ya fi (kowanne) saboda albarkar wannan rana da aka haifi Manzon Allah (SAW) muka samu wadannan ni’imomi. Kuma ba mu kadai muke wannan murna ba. Allah ya gaya mana duk Annabawa ga su a cikin Al’kur’ani suna murna da kwanakinsu. Annabi Yahya (AS) Allah ne ma da kansa ya fadi murna a kwanakinsa (wa salamun alaihi yauma wulida wa yauma yamutu wa yauma yub’asu hayya…
“Akwai Annabi Isah (AS) da Allah ya fadi duk yadda aka yi lokacin haihuwarsa. Kuma mun gode Allah, duk an ruwaito mana abubuwan da mahaifiyar Manzon Allah (SAW) ta gani da abubuwan da suka faru a lokacin haihuwarsa (SAW). Kowa a cikinmu musulmi ya tabbatar Annabi Muhammadu (SAW) ya fi Annabi Isah (AS), mahaifiyar Annabi (SAW) ta fi ta Annabi Isah (AS), to ya za mu yarda da wancan (na Annabi Isah AS) sannan mu kasa yarda da wannan (na Annabi SAW)?” Ya tambaya.
Sheikh Isma’ila Mai Diwani ya kuma bayyana yadda maulidi yake kara dankon soyayya da zumunci da ‘yan’uwantaka a tsakanin al’ummar musulmi, inda ya nunar da cewa ko a maulidin na Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Sakkwato, mutane daga sassan Nijeriya har ma da kasashe makota sun halarta, inda suka hadu wuri daya, suka gana da juna cikin farin ciki, kana ga abubuwa na tarihi da dabi’un Manzon Allah (SAW) da ake koyarwa a wurin maulidi, “wanda daga ciki ko daya muka dauka a cikin dabi’unsa (SAW) muka yi koyi alheri zai faru ya yadu a bayan kasa.”
Tun da farko a jawabinsa na maraba da baki da sauran mahalarta, jagoran shirya Maulidin, Sayyadi Abubakar Umar Sakatare ya gode wa Sheikh Isma’ila Umar Almaddah bisa taimakon da yake yi musu a zahiri da badini cikin dukkan al’amuransu na Allah.
“Wallahi mukan rasa inda za mu yi da jagoranmu Shehu Isma’ila Umar Almaddah saboda jin dadi, duk hidimar da ake cewa ‘yan Sakkwato sun yi lokacin maulidi, idan mun je Kaduna sai a kashe mana kuma har a biyo mu canji. Ya Shehu muna neman a yi mana afuwa saboda takaitawa.” In ji shi.
Daga cikin manyan bakin da suka halarta, akwai Farfesa Yahaya Al-amin (Limamin Kasausawa) da Dakta Aminu Abdullahi Sufi da Sakataren Majalisar Sufayen Darikar Tijjaniyya, Alhaji Lawal Abdullahi Maigaskiya da Malam Tukur Gobirare da Khalifah Bello Balarabe Gobirawa da sauransu.