A shekarar 2013, ƙasar Sin ta gabatar da shirin shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya ko BRI a taƙaice, a matsayin wani gagarumin shiri na raya ababen more rayuwa, domin haɗa ƙasashen Asiya da Turai da Afirka ta hanyar hada-hadar ayyuka daban-daban. Bisa ƙididdigar da bankin duniya ya bayar, BRI ya ƙunshi tattalin arzikin ƙasashe 71, ciki har da ƙasar Sin, wanda ke da alhakin kashi 40 cikin 100 na kayayyakin da ake fitarwa a duniya, da kashi 35 cikin 100 na jarin waje kai tsaye a duniya.
Ƙasashe masu tasowa suna kallon BRI a matsayin tushen samar da kuɗaɗe, zuba jari, kasuwanci, da samar da ababen more rayuwa wanda zai iya bunƙasa ci gaban tattalin arzikinsu da ci gabansu. Kaza lika, wasu ƙasashen suna kallon BRI a matsayin wata hanya ta daidaita shingaye dake kawo cikas ga ci gaban ƙasashe masu tasowa da wasu yankunan kamar Amurka ko Japan suka kafa. BRI na samar da wasu hanyoyin samar da tsaro, kwanciyar hankali, da dogaro ga waɗannan ƙasashe, musamman a yankunan da suke fuskantar takaddamar tsakanin juna, da gabar siyasa, ko matsin lamba daga waje.
- Sin Ta Kafa Kyakkyawan Misali A Fannin Kare Hakkokin Bil Adama
- Sin Ta Yi Kira Da A Tsagaita Bude Wuta A Tsakanin Palasdinu Da Isra’ila Ba Tare Da Wani Jinkiri Ba
Har ila yau, ƙungiyar ta BRI ta samar da haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasa da ƙasa a fannonin kimiyya, fasaha, ilimi, da al’adu, da samar da sabbin damammaki na ƙirƙire-ƙirƙire, da bunƙasa hazaka, yayin da kayayyakin fasahohin da ƙasar Sin ke fitarwa zuwa ƙasashen BRI ya ƙaru da kashi 10.9 cikin dari a duk shekara, kuma kayayyakin fasaha daga ƙasashen BRI suka ƙaru da kashi 20.1 a kowace shekara.
A cikin shekaru 10 da suka gabata, an gudanar da ayyukan hadin gwiwa fiye da 3000 don gina shawarar “ziri daya da hanya daya”, wadanda suka kai ga zuba jarin triliyoyin dalar Amurka. Ya zuwa karshen watan Yunin wannan shekarar 2023, Sin ta sanya hannu kan takardun hadin gwiwa fiye da 200 kan shirin raya shawarar “ziri daya da hanya daya” tare da kasashe fiye da 150 da kuma kungiyoyi fiye da 30.
Binciken bankin duniya ya nuna cewa, gudanar da shawarar “ziri daya da hanya daya” yadda ya kamata, zai kara habaka cinikayya tsakanin kasashen da suka amince da shawarar zuwa 4.1%, kana nan da shekarar 2030, ana sa ran cewa, shawarar za ta samarwa duniya kudaden shiga har dalar Amurka tiriliyan 1.6 a duk shekara. Kuma ana sa ran za ta cire mutane miliyan 7.6 daga kasashe masu hadin gwiwa daga matsanancin talauci.
A cikin waɗannan shekaru 10 da suka gabata, BRI ya ba da gudummawa sosai ga ci gaban GDP na duniya, musamman ga ƙasar Sin da sauran ƙasashen da ke halartar taron. Alkaluman ƙididdiga sun yi hasashen cewa, BRI na iya ƙara yawan GDPn duniya da kashi 0.7 bisa ɗari ya zuwa shekarar 2030 da kuma kashi 2.6 bisa ɗari ya zuwa shekarar 2050, kuma GDP na ƙasar Sin na iya ƙaruwa da kashi 3.4 cikin 100 nan da shekarar 2030 da kuma kashi 5.3 nan da shekarar 2050, sakamakon bunƙasuwar BRI.
Abinda Ya Sa Ƙasashen Afirka Ke Maraba Da Shirin Shawarar BRI
Afirka ta kasance wani muhimmin ɓangare na ƙoƙarin da ƙasar Sin ke yi game da shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”, saboda buƙatunta na ababen more rayuwa kamar su layin dogo, hanyoyi da makamashi, wanda har yanzu ake kallon a matsayin wani babban shinge na ci gaba a yankin. A shekarar 2020, kashi 43 cikin 100 na ‘yan Afirka ne kawai ke samun wutar lantarki, kashi 48 cikin 100 ne ke da shimfiɗaɗun hanyoyin sufurin mota, sannan kashi 6 na filayen noma ne ake iya sarrafawa. Ƙasar Sin ta fara ayyukan zuba jari da dama a yankin gabashin Afirka, bisa la’akari da damar samun tashar jiragen ruwa da kuma buƙatar layin dogo da tituna. An ci gaba da faɗaɗa manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa zuwa kudu da arewacin Afirka, kamar gadar Maputo-Katembe ta Mozambique da titin Cherchell Ring Expressway na Aljeriya. Ayyukan shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” a Afirka sun fi mayar da hankali kan sufuri da wutar lantarki, da layukan dogo na ƙasa da ƙasa, da tashoshin jiragen ruwa, da makamashin ruwa zuwa wutar lantarki, da samar da ruwan sha da tsaftar muhalli, da sauran shirye-shirye masu alaƙa.
Bayan haka, jarin da ƙasar Sin ta zuba a yankin ya ƙaru sosai tun daga farkon shekarar 2000, inda adadin kuɗaɗen da gwamnatin ƙasar Sin da kamfanonin ƙasar suka kashe ya kai dalar Amurka biliyan 23 a shekarar 2020. Yanzu ƙasar Sin ita ce ƙasar da ta fi ba da gudummawar ayyukan more ababen rayuwa a Afirka, inda ta ba da tallafin kuɗi kusan kashi biyar na dukkan ayyukan samar da ababen more rayuwa da gudanar da kashi uku na waɗannan ayyukan. Wani rahoton McKinsey & Company ya yi kiyasin cewa sama da kamfanoni 10,000 na ƙasar Sin ne ke aiki a Afirka, inda kashi 90 cikin 100 na masu zaman kansu ne. Bincike da dama sun nuna cewa, jarin da ƙasar Sin ta zuba ya yi tasiri mai kyau a Afirka. A cewar wani shirin bincike na Afirka na Johns Hopkins, ƙasashen gabashin Afirka kaɗai sun karɓi rancen kuɗi sama da dala biliyan 29 daga ƙasar Sin don gudanar da ayyuka daban-daban.
Domin gudanar da mafi yawa daga cikin ayyukan gine-ginen, ƙasar Sin ta tura ma’aikatan Sinawa da dama zuwa ƙasashe masu tasowa. Baya ga ayyukan tattalin arziki, ƙasar Sin ta kuma tsara shirin na shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” a matsayin wata dama ta ƙulla alaƙar al’adu tsakanin Afirka da Sin.
Fa’idar Shawarar “Ziri Ɗaya Da Hanya Ɗaya” Ga Kasashen Afirka
Samun ruwan sha mai tsafta ya kasance babban ciwon kai ga Senegal, domin yankinta na arewa yana kusa da hamadar sahara, kuma ɓangaren yammacinta shima ya kasance Sahara. A kowace rana a Balin, wani ƙaramin ƙauye a ƙasar Senegal, mutane su kan tashi da sassafe don yin layin ɗibar ruwa daga rijiyar ƙauyen. Wasu sun kan yi tafiya fiye da kilomita biyu kafin su isa rijiyar. Ababen more rayuwa a yankin sun lalace kuma an kasa biyan buƙatun jama’ar ƙauyen tsawon shekaru da yawa.
Al’amura sun canja a shekarar 2018. A ƙarƙashin aikin hako rijiyoyin karkara da gwamnatin ƙasar Sin ta samar ƙarƙashin shirin shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” (BRI), an shimfida bututun ruwa mai tsayin sama da kilomita 1,800, wanda ya samar da ruwan sha ga al’ummar ƙasar Senegal miliyan biyu. Kuma ta samar da ayyukan yi ga al’ummar yankin sama da 3,000.
A ƙasar Angola, inda mafi yawan yankuna da mutane ba sa samun ruwan famfo, motocin dakon ruwa ne kawai za su iya dogaro da su domin amfanin yau da kullum, kuma dole su biya kuɗi. A watan Yunin shekarar 2022, kamfanin shimfida layin dogo na ƙasar Sin (CRCC) ya kammala aikin samar da ruwan sha na Cabinda a Angola, kuma jama’ar ƙasar da dama sun samu ruwan famfo a karon farko a rayuwarsu. “Muna jinjinawa ƙasar Sin! Muna godiya da zuwanku don taimaka mana!” Waɗannan su ne kalaman mazauna 600,000 waɗanda suka ci gajiyar ayyukan.
Da zarar an sami biyan buƙatu na yau da kullun, ana sa ran ƙarin ci gaba. Ga ƙasar Kenya, samun sabon layin dogo ya kasance mafarki ne na tsawon ƙarni. Titin jirgin ƙasa mai auna mita da turawan mulkin mallaka suka gina sama da shekaru ɗari da suka wuce ya lalace yayin da ƙasar ta kasance ba tare da isassun ƙarfin sufuri ba. Ci gaban ƙasar gaba ɗaya ya kasance cikin kangi har zuwa lokacin da aka fara aikin titin jirgin ƙasa daga Mombasa zuwa Nairobi a watan Mayun 2017. Wannan gagarumin aikin dake ƙarƙashin tsarin BRI ya rage yawan lokacin tafiya daga Mombasa zuwa Nairobi zuwa sa’o’i 4.5 tare da rage kuɗin tafiyar da kashi 40 cikin ɗari. Yayin da sama da kamfanoni 1,000 na cikin gida suka farfado, wannan layin dogo ya ba da gudummawar kashi 2 cikin 100 ga ci gaban GDP na Kenya, ya kuma ba da bunkasuwar yawon shaƙatawa a Kenya.
Ba wai ƙasar gaba dayanta kadai ta amfana sosai daga BRI ba, amma har da sauƙaƙa samun damammaki ga duk talakan da abin ya shafa. ‘Yan kwangilar ƙasar Sin sun yi musayar fasahohi ta hanyoyi daban-daban, sun baiwa dubun-dubatar jama’ar ƙasar damar samun fasahohin sana’o’i, da samar da guraben aikin yi kusan 46,000 a cikin gida. Kafin a fara aikin titin dogo na Mombasa zuwa Nairobi, babu wani tunanin cewa mace za ta iya tuƙa jirgin ƙasa a Kenya. Amma a baya-bayan nan mata bakwai na farko direbobin jirgin ƙasa da kamfanin na ƙasar Sin ya horar da su a yanzu sun zama kwararrun matuƙa jirgin ƙasa. Shahararrun kafafen yada labarai na ƙasar Kenya sun ba da labarin wadannan direbobin mata, kuma sun zama abin ambato na yau da kulllun.
A game da ƙasar Burundi kuwa, ƙasa mafi ƙarancin ci gaba, wadda ta shiga ƙungiyar BRI a shekarar 2018 tare da haɗin gwiwar aikin gona a matsayin mafari, ƙasar ta gabashin Afirka ta samu babban ci gaba daga ƙoƙarin da ƙasar Sin ke jagoranta. Gazawar Burundi shekaru da dama da suka yi na rashin iya bullowa da fa’idar aikin gona, ya ba da gudummawa ga al’ummar gabashin Afirka ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya dake fama da matsalar ƙarancin abinci.
Amma, tun bayan da ƙasar ta ƙulla alaƙa da ƙasar Sin a ƙarƙashin shirin BRI, wanda ya ƙara inganta haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasashen biyu a fannin noma, a cikin shekaru biyar da suka gabata, an samu ci gaba sosai a fannin noma da kiwo, musamman a fannin noman shinkafa wanda ya ƙara inganta wadatar abinci da tsaro.
A matsayin ɗaya daga cikin muhimman abinci na ƙasar Burundi, shekaru da dama da aka samu ƙarancin amfanin noman shinkafa ya haddasa matsalar ƙarancin abinci. Amma, ta hanyar yin aiki tare da BRI, ya zuwa yanzu ƙasar Burundi ta karbi bakuncin manyan kwararru biyar a fannin aikin gona daga ƙasar Sin, kwararrun na ƙasar Sin sun gudanar da bincike da gwaje-gwaje iri-iri, sun gudanar da tafiye-tafiye a dukkan larduna 15 da ake noman shinkafa a ƙasar Burundi, kuma sun samu nasarar zabo tare da gabatar wa manoma da wasu nau’ikan iri na shinkafa takwas da suka dace da yanayi da muhallin ƙasar. Godiya ga wannan ƙoƙarce-ƙoƙarce, rashin amfanin gona ko ƙarancin amfanin gona wanda galibi ana danganta shi da annobar shinkafa a yankunan tsaunuka na Burundi ya zama tarihi.
Ƙasashen Afirka, kama daga Uganda, Aljeriya, Sudan, Tanzaniya duk suna cin gajiyar shawarar BRI a fannoni ababen more rayuwa daban-daban.
Wasu Ayyukan BRI A Najeriya A takaice
Tashar jiragen ruwa ta Lekki, wani shiri ne BRI a yammacin Afirka wanda Kamfanin Harbour na ƙasar Sin ya gina, zai iya sarrafa kwantena miliyan 1.2 a duk shekara. Hakan zai ƙara ƙarfin sarrafa kwantena ƙasar da kashi 80 cikin 100, wanda hakan zai sa ta kasance tashar jiragen ruwa mafi girma a Najeriya.
A watan Janairu, layin dogo na farko da aka samar mai aiki da wutar lantarki a yammacin Afirka ya fara aiki a Legas. Aikin wanda kamfanin CCECC ya shimfida, tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana shi a matsayin aiki mai dauke da tarihi, domin zai sauƙaƙa cunkoson ababen hawa, da inganta rayuwa.
Kaza lika, aikin layin dogo na Lagos-Ibadan Standard Gauge SGR, wanda ya haɗa Legas zuwa Ibadan, babban birnin masana’antu a kudu maso yammacin Najeriya, an fara aiki ne a watan Yunin 2021. Shi ne SGR na zamani mai layin biyu na farko a yammacin Afirka, da kuma wani ɓangare na SGR mai tsawon kilomita 1,343 daga Legas zuwa Kano, wanda ake kan ginawa. Idan an kammala aikin layin dogon zai zama babban jigo a Najeriya, inda zai maye gurbin tsohon layin dogo da Turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka gina a karnin da ya gabata.
A birnin Kano da ke arewacin ƙasar kuma, ana aikin wani layin dogo da ya haɗa ƙasar daga Kano zuwa Maradi mai tsawon kilomita 387, zai sauƙaƙa alaƙar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
A wannan makon ne an gudanar da taron haɗin gwiwa tsakanin ƙasa da ƙasa na shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya karo na uku ko BRF a takaice, da ya haɗa ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma bikin cika shekaru 10 da kafa ƙungiyar BRI. Taron wata muhimmiyar hanya ce ga masu tsara manufofi, abokan raya ƙasa da ƙasa, da sauran masu ruwa da tsaki, don yin musayar kwarewa, da buɗe sabbin damammaki na samun bunƙasuwa a ƙarƙashin ƙoƙarin da ƙasar Sin ke jagoranta na tinkarar ƙalubalen duniya. (Muhammed Yahaya)