Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa hukuncin kotu kan ‘yan takara da rikice-rikicen da ke faruwa a jihohin suna matukar kawo mana cikas game da shirye-shiryen hukumar na gudanar da sahihin zabe a ranar 11 ga Nuwambar 2023.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ya bayyana hakan a wani taro tare da jam’iyyun siyasa wanda ya gudana a Abuja.
- Gobe Za A Tsame Duk Ma’aikacin Tarayya Da Ba Ya Cikin Tsarin IPPIS Daga Biyan Albashi
- Gwamnatin Tinubu Za Ta Muhimmanta Amfani Da Na’urorin Zamani A Gidajen Rediyo Da Talabijin – Minista
Ya nuna matukar damuwarsa game da rikice-rikicen da suke tasowa a wadannan jihohi guda uku a tsakanin magoya bayan jam’iyya da ‘yan takara, ya yi gargadin cewa babu yadda za a yi a iya gudanar da sahihin zabe babu cikakken zaman lafiya.
“Sake buga kayayyaki zabe bisa bin umarnin hukuncin kotu cikin kankanin lokaci ba wai tsada ba ne kawai har ma yana shafar ayyukan hukumar. Ko da yake hukumar ta riga ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar jihohin uku, amma umarnin kotu guda hudu da ya tilasta mana sake duba jerin sunayen.
“Wadannan canje-canjen sun bayyana a cikin sabunta jerin jam’iyyu da ‘yan takara a shafinmu na sada zumunta. Daukar wannan hukuncin ba tare da la’akari da abin da zai janyo ya shafi hukumar da ‘yan takarar ko jam’iyyunsu.
“Yayin da yakin neman zabe ke ci gaba da dagula lamura, hukumar ta sake jaddada damuwarta game da yawaitar tashe-tashen hankula a jihohin uku da suka hada da jam’iyyu da ‘yan takara. Ina so in tunatar da ku a matsayinku na shugabannin jam’iyya cewa zabuka na gaskiya da adalci ba zai yiwu ba sai cikin yanayi na zaman lafiya,” in ji Yakubu.
Shugaban INEC ya ce zaben wani tsari ne da ya kunshi Bil’adama a matsayin masu jefa kuri’a, masu sa ido da kuma kafafen yada labarai wadanda tsaron lafiyarsu ya shafi hukumar.
Yakubu ya ce zabukan a jihohin guda uku yana da matukar rudani a wajen gudanarwa.
Ya kara da cewa a daidai lokacin da ya rage makwanni biyu kacal a gudanar da zaben, INEC na gab da kammala shirye-shiryenta kuma wannan shi ne karo na farko da hukumar za ta gudanar da zabukan gwamnoni guda uku a lokaci guda a yankuna daban-daban.
“Hakan zai yiwu ne a daidai lokacin da masu rike da mukaman suke cika wa’adin mulkisu wanda bai wuce kwanaki 150 ba ko kuma bayan kwanaki 30 kafin cikar wa’adin mulkinsu a gudanar da zabe kamar yadda sashe na 178 (2) na kunkundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 ya tanada,” in ji shi.
Da yake mayar da martani a madadin jam’iyyun siyasar da suka yi rajista, shugaban kungiyar IPAC, Injiniya Yabagi Sani, ya ce domin tabbatar da amincewar ‘yan kasa, dole ne INEC ta ci gaba da nuna rashin son kai da gaskiya da kuma jajircewa wajen gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci.
Ya kuma bukaci INEC da ta yi aiki tukuru tare da hada kai da jami’an tsaro wajen dakile matsalar tsaro da ‘yan siyasa masu daukar siyasa a mutu ko a yi rai.