Wani dalibi a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta Jihar Kaduna, mai suna Abdullahi Ibrahim, ya shiga hannun jami’an tsaron NSCDC a Jihar Bauchi bisa zargin kashe wani matashi dan shekara 17 da haihuwa.
An ce wanda ake zargin ya yaudari matashin dalibin sakandaren ne da hotonsa tsirara tare da hilatarsa kan ya same shi domin aikata luwadi.
- CMG Ta Gabatar Da bukukuwan Baje Kolin Al’adun Sin Na Musamman A “Palace of Nations” Da Kasar Masar
- Gwamnatin Tarayya Ta Kara Karbo Bashin Dala Biliyan 3.45 Daga Bankin Duniya
Kwamandan NSCDC reshen Jihar Bauchi, Ilelaboye Oyejide, ya shaida wa manema labarai yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a shalkwatar rundunar, ya ce lamarin ya faru ne a garin Misau da ke Karamar Hukumar Misau ta jihar.
Oyejide ya ce rundunar ta samu labarin wani laifin aikata kisan kai cewa wani dalibi dan shekara 17 mai suna Umar Usman, mazaunin Misau, an same shi a nannade cikin wata riga da aka jefar a kan hanyar Misau.
Ya bayyana cewa, “A ranar 20 ga Oktoba, 2023, an tsinci gawar Umar Usman a yashe an lullube da farin kyalle da aka jefar da ita a mashigar Misau.
“Ba tare da bata lokaci ba aka kai gawar babban asibitin Misau inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa. An mika gawarsa ga ’yan uwa don yi musu jana’iza.
“Bayan cikakken bincike da jami’an suka yi, an kama wani da ake zargi mai suna Abdullahi Ibrahim, dalibi mai matakin digiri 500 a fannin likitan dabbobi na ABU Zaria.
“Mun fahimci cewa akwai tattaunawa tsakanin wanda ake zargin, Ibrahim da marigayin, Usman. A cikin hirar mun ga inda wanda ake zargin ya yaudari marigayin da soyayyar luwadi kuma ya nuna masa hotonsa tsirara.
“Lokacin da Usman ya je ya same shi ba mu san dai yadda aka yi ba, amma dai mun samu a jikinsa an soka masa wuka a cikinsa yayin da muka tsinci gawar nannade da farin kyalle an jefar da ita.” Ya ce yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.