Tun bayan cire tallafin mai, hauhawar farashin kayyaki ta jefa al’umma cikin radadin matsain tattalin arziki wanda a sakamakon haka gwamnati ta fito da tsare-tsare don kawo agaji ga al’umma kan halin da suke ciki. Daga ciki akwai shirin bayar da tallafin kudi Naira dubu ashirin da biyar (25, 000) har na tsawon watanin uku.
Sabuwar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da cewa za ta biya mutanan da suke cikin shirin rage fatara na RRR nan ba da jimawa ba. Shiri ne da aka rufe rijistarsa tun a tsohuwar gwamnati, biya kawai ya rage amma kuma har zuwa hada wannan rahoto shiru kake ji kamar an shuka dussa.
- Me Ya Hana Amurka Ta Ce “A Tsagaita Bude Wuta”?
- Sin Ta Yi Kira Da A Hada Kai Wajen Samar Da Tsaron Fasahar AI
A karkashin Shirin Gwamnatin Tinubu na ‘Conditional Cash transfer’, Ministar Jin kai da yaki da Fatara, Dakta Betta Edu, ta ce za a rika biyan magidanta miliyan 15 tallafin kudi na Naira 25,000.00 na tsawon watanni uku wanda zai kama Naira 75,000 ke nan.
Sai dai tsare-tsaren Shirin na yanzu sun bambanta da na tsohuwar gwamnati, inda a sabon shirin ‘Conditional Cash Transfer’ hatta talakawan da ba su da lambar shaidar dan kasa da ta hade asusun banki wuri daya su ma za su iya cin gajiyar shirin mutukar suna da lambar waya wadda za a bude asusu da ita.
Domin nasarar shirin da takwarorinsa na yaki da talauci, Gwamnatin Tinubu ta kaddamar da gidauniya ta musamman da za a ajiye fiye da Dala Biliyan 5 a duk shekara.
Sai dai kuma a wani mataki na rashin gane inda aka dosa a shirin, Majalisar Wakilai ta yanke shawarar gayyatar Dakta Betta Edu don ta yi bayani a kan tsare-tsaren da za su yi amfani da su wajen rabon tallafin.
Wannan ya biyo bayan kudirin da dan majalisa daga Jihar Osun, Morufu Adebayo ya gabatar ne a zauren majalisar a tsakiyar makon nan.
Shirin wanda zai ci kimanin Naira Tiriliyan 1.1, yana daya daga cikin yarjeniyoyi 15 da aka cimma a tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago a ranar 2 ga Oktobar da ta gabata.
‘Yan majalisar dai sun ce bai kamata a bar su a gefe ba wajen aiwatar da wannan shirin saboda su ne suke kusa da jama’a, sun san abin da ya kamata a yi, don haka suka bukaci a yi musu bayanin yadda za a gabatar da shirin dalla-dalla.
Saboda rashin sanin alkiblar da Shirin ya dosa, wakilanmu na wasu jihohi sun binciko yadda lamarin rabon tallafin na Naira 25,000 ga talakawa yake a yankunansu inda rahotanni suka bambanta, wasu sun bayyana cewa, zuwa yanzu babu duriyar shirin a jihohinsu.
Kano
Tallafin Rage Radadi A Kano, Flashing Ne Kawai- Amb. Dandago
A Jihar Kano, ba a ji duriyar wannan tallafi ba, sai dai wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya shelanta raba wa kowace Jiha Naira Biliyan biyar-biyar domin sayen kayan abinci don raba wa jama’a.
Gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusif ya bayyana cewa sun tanadi Tirelolin shinkafa da Masara Sama da 100 Wanda aka tsara raba wa al’umma.
Gwani Musa Hamza Falaki, guda cikin ‘yan kwamitin rabon tallafin, ya bayyana cewa Shirin da Gwamnatin Kano ta yi kan yadda ake raba tallafin ya zarta na sauran jihohin tsafta, domin babu siyasa acikinsa, kasancewar an tsara a kowace mazaba cikin mazabu dari Hudu da doriya da ke Jihar Kano za a raba buhun shinkafa 400 haka ita ma Masara buhu 400.
Gwani Falaki ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Kano nada yakinin cewa wannan tallafi zai Isa hannun wadanda aka tsara domin su, musamman ganin har kowacce mazaba ake kai kayan kuma a raba su a gaban masu ruwa da tsaki.
Shi kuwa a nasa bangaren Amb. Mansur Haruna Dandago ya bayyana cewa, rabon tallafin da ake a Kano ‘Flashing’ ne kawai, domin yanzu haka cikin mutum Dubu a Kano da kyar za ka samu mutum biyar da suka taba ganin irin wannan tallafin da Gwamnatin Kano ke ta kumajin cewa tana raba wa talakawa. Wani abin takaici ma in ji Dandago shi ne yadda idan aka bai wa mutum buhun shinkafa, ga sunan shinkafa ce baro-baro a jikin buhun, ga kuma hoton gwamna, amma da an bude sai a tarar Masara ce a cikin buhun ba shinkafa ba.
Bugu da kari, wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa akwai mazaba guda ma da ake zargin nasu kason ya yi batan dabo.
BAUCHI DA GOMBE
Babu Duriyar Shirin A Jihar Bauchi
A jihar Bauchi dai har lokacin hada wannan rahoto, shirin ba da tallafin Naira dubu ashirin da biyar ga talawa da Gwamnatin tarayya ta yunkuri domin yinsa bai kankama ba.
Kazalika, wata majiya daga ma’aikatar kula da harkokin jin kai da walwar Jama’a ta jihar Bauchi ta ce har zuwa yanzu ba a fara komai kan shirin ba.
“Har yanzu dai babu wani bayani kan wannan shirin ba a fara ba zuwa yanzu. Amma da zarar aka fara za mu sanar da ku,” cewar majiyarmu.
Kazalika, kusan haka batun ma yake a jihar Gombe domin kuwa har zuwa yanzu babu wani matakin da aka dauka na fara aiwatar da shirin yayin da talalawan ke zaman jiran tallafi daga wajen Gwamnatin tarayya.
Wani mai karamin karfi da muka zanta da shi a jihar Bauchi, Malam Ahmad Rashad, ya ce, “To mu dai muna jin wai-wai, amma da za a ce za a raba tallafin ko ma nawa ne gaskiya in dai an tabbatar talakawa irinmu ne ke samu hakan zai rage radadi a cikin al’umma, domin ni yanzu jari na ma bai taka kara ya karya ba, kuma akwai irina da dama da tallafi ko na nawa ne zai yi matukar taimakonmu.
“Don haka muna rokon Gwamnatin da ta duba ta tabbatar da wannan shirin da muke jin waiwai dinsa ya tabbata,” ya shaida
Kebbi
An Fara Tantance Al’umma
Dangane da shirin tallafin na “Cash Transfer” a Jihar Kebbi, wata majiya mai karfi ta tabbtar wa wakilinmu cewa” an tantance sunayen maigidanta da marasa karfi mutum dubu takwas (8,000.00) da ke a fadin kananan hukumomin 21 a jihar.
Majiyar ta kara ta cewa a halin yanzu ma’aikatar jinkai da rage fatara ta ba da umurnin sake tantancewa da tabbatar da sunayen maigidanta da marasa karfi a Jihar Kebbi bisa ga bayyanansu da aka dauka tun a farkon wannan shekarar.
A halin yanzu wani maigadanci mai suna Malam Suleiman Saidu da ke a unguwar Badariya a cikin karamar hukumar mulki ta Birnin Kebbi ya ce ” gaskiya ne ana kan tantancewa da tabbatar da bayyanan mutune ya yi daidai domin a satin da ya gabata jami’an da ke tantance mutane sun zo gidana inda suka kara tabbatar da bayyanan da na bayar.
Kazalika, majiyar ta ce” bayan an kammala tantance mutane za a turo wa sashen kula da walwalar jama’a na kasa (NASSCO) inda bayan su ma sun kammala nasu aikin za su turo wa sashen rabon kudin, ‘National Cash Transfer (NCTO)’.
Zamfara
Ba A San Halin Da Shirin Ke Ciki A Jihar Zamfara Ba
A binciken da LEADERSHIP HAUSA ta yi a kan ba Ma’aikata tallafin N25,000, na tsawon wata uku da gwanatin Tarayya ta ayyana za ta fara daga watan jiya ga jihohin dan rage masu radadi a kan halin da al’umma ke ciki na matsin rayuwa.
A Jihar Zamfara da, talakawa sun bayyana farin cikinsu kan wannan tallafin don a tunaninsu Gwamna Dauda Lawal yana bin tsari da ka’ida a duk harkokin da gwamnati ke yi a jihar.
Wani ma’akacin jihar da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, gwamnan da ya gaji albashin wata uku ya biya a cikin wata guda, “ina ga karin tallafin wanda bai kai albashi ba? dan haka Ina da tabbas Gwamna Dauda zai ba da tallafin da yardar Allah.”
A kan haka wakilinmu ya tuntubi Shugaban kugiyar kwadago na Jihar Kwared Sani Haliru, a kan batun da kuma wane shiri suka yi da gwamnatin don fara cin gajiyar tallafin, inda ya ce zai kira ta waya amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai kira ba.
A ta bangaren gwamnati kuwa, wakilinmu ya kira Daraktan Yada Labarai na Gwamna Dauda, Nuhu Salihu Anka inda ya bayyana cewa, a cikin satin nan ne gwamnoni za su yi taro a Abuja kan matsayarsu wajan rabon tallafin.
Borno da Yobe
Daga Jihohin Borno da Yobe kuwa, Ministar Jin Kai, Dakta Betta ta bayyana cewa a cikin adadin ‘yan Nijeriya miliyan 15, kimanin sama da magidanta miliyan 8 da digo 3 daga jihohin Borno, Adamawa da Yobe, tare da wasu jihohin da ke Arewa ta Tsakiya da makamantan su za su ci gajiyar Shirin na rabon tallafin kudi.
LEADERSHIP HAUSA ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen jin ra’ayoyin al’ummar jihohin Borno da Yobe, don jin ko shirin ya kankama, inda daga bisani jama’a da dama suka bayyana cewa ba su da masaniya kan shirin, yayin da wani sashe kuma suka nuna rashin gamsuwarsu kan batun, tare da bayyana cewa an sha yin ruwa kasa na shanyewa.
Malam Usman Muhammad Damaturu ya bayyana cewa, “kwanan baya mun samu labarin ana cika fom din bayar da tallafin 25,000 wanda Gwamnatin Tarayya za ta bayar, amma har yanzu ba mu gani a kasa ba. Amma da dama matasanmu sun cika ta hanyar yanar gizo, amma gaskiya har yanzu babu labarin komai.”
A can ma jihar Borno ba ta canja zani ba, inda Malam Abubakar Goni ya bayyana nashi ra’ayin da cewa, “Gaskiya na cika fom din shirin Gwamnatin Tarayya na bayar da tallafin, kuma muna nan mun zuba ido tare da jira. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, mutane kalilan ne suka samu damar shiga cikin tsarin a nan jihar Borno sakamakon sanyin gwiwar da suke da shi dangane da al’amarin tallafin gwamnati, wanda ba kasafai talaka ke samu ba.”
Ita dai ma’aikatar ta jin kai, ta ce har yanzu tana aikin tantancewa ne, shi ya sa ba a fara rabon ba. Ko a wannan makon, ma’aikatar ta shawarci jama’a su yi watsi da masu cewa ana cike wani fom ta intanet na neman tallafin tare da jadda cewa ‘yan damfara ne suka kirkiri wannan.