Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu a harin ‘yan fashi da makami a ranar 11 ga watan Mayun 2022 a Otal din Mambillah, Owutu, Ikorodu a jihar Legas.
Wani mai taimaka wa Gwamna, Babajide Sanwo-Olu, kan harkokin yada labarai, Jibrin Gawat, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter da aka tabbatar a ranar Alhamis.
- ‘Yan Sanda Sun Cafke Barayin Ragon Layya 2 A Ogun
- ‘Yan Sanda Sun Kama Wata Mata Da Ta Sace Yarinya A Anambra
Gawat ya rubuta cewa: “Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wasu mashahuran mutane shida da ake zargi da hannu a harin fashi da makami a ranar 11 ga Mayu, 2022 a Otal din Mambillah, Owutu, Ikorodu.”
Idan ba a manta ba a ranar Laraba 11 ga watan Mayun 2022 ne ‘yan fashi da makami suka kashe wani jami’in tsaro mai suna Peter a lokacin da suka kai hari a otal din.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, a lokacin da ‘yan fashin suka kai farmaki otal din da misalin karfe 2:40 na safiyar ranar ma’aikata da kwastomomi na barci.
An bayyana cewa da yawa sun farka ne a lokacin da barayin suka shiga dakuna inda suka yi musu fashi da makami.
Daga cikin wadanda abin ya shafa har da jami’an hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB uku, wadanda aka ce ma’aikata ne a otal din.